A ran 8 ga wata, ya kasance da sauran shekaru biyu da za a fara yin wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. A wannan rana ce, a nan birnin Beijing, gidan rediyo kasar Sin ya bude wani zango na musamman domin watsa shirye-shiryensa kan wasannin Olympic na Beijing a dare da rana cikin harsuna 9 kamar Ingilishi da Faransanci da Spananci da Rashanci da sauransu. Wato ke nan a karo na farko ne kasar Sin ta bude wani zango na musamman domin watsa labaru a kan wasannin Olympic na Beijing da ayyukan share fage cikin harsunan kasashe daban daban.
A wannan rana da maraice, a nan birnin Beijing, gidan rediyo kasar Sin ya shirya bikin bude wannan zango na musamman domin fara watsa shirye-shiryensa kan wasannin Olympic na Beijing. Shirye-shiryen za su shafi labarun wasannin motsa jiki da na wasannin Olympic da hadimomin zaman rayuwa da filayen musamman na wasannin Olympic dangane da harkokin siyasa da na tattalin arziki da al'adu da yawon shakatawa na kasar Sin da kuma Ingilishin wasannin Olympic.
Malam Wang Gengnian, shugaban gidan rediyon kasar Sin ya yi jawabi a gun bikin budewar nan cewa, "yayin da ranar da za a fara wasannin Olympic na Beijing ke kara kusantowa, gasannin wasannin motsa jiki da ake yi a Beijing kullum sai kara karuwa suke yi, haka nan kuma masu yawon shakatawa na kasashen waje wadanda ke zuwa birnin Beijing ma kullum sai kara karuwa suke yi. Duk wadannan baki 'yan kasashen ketare suna alla- alla su fahimci birnin Beijing da kasar Sin da labarun wasannin Olympic na Beijing cikin harusnansu ta hanyar kafofin watsa labaru. Sabo da haka gidan rediyon kasar Sin ya bude wannan zango na musamman domin watsa shirye-shiryensa kan wasannin Olympci na Beijing cikin harsuna daban daban."
Gidan rediyo kasar Sin ya sami babban goyon baya daga wajen kwamitin kula da harkokin shirya wasannin Olympic na Beijing wajen bude wannan zango na musamman. Malam Liu Jingmin, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin kuma mataimakin magajin gari na Beijing ya halarci bikin bude wannan zango na musamman, inda ya bayyana cewa, "gidan rediyo kasar Sin wani babban gidan rediyo na kasar Sin ne da ke watsa labaru ga kasashen waje. Ya kware sosai wajen watsa shirye-shiryensa cikin harsuna da yawa. Bude zango na musamman da gidan rediyo kasar Sin ya yi a yau domin watsa shirye-shiryensa kan wasannin Olympic na Beijing, zai taka muhimmiyar rawa wajen yayata wasannin Olympic na Beijing, da nuna kyakkyawan halin kasar Sin."
Malam Jacques Rogge, shugaban hukumar wasannin Olympic ta duniya ya taya gidan rediyo kasar Sin murna, yayin da yake shirye bude wannan zango na musamman don watsa shirye-shirye kan wasannin Olympic na Beijing. Ya ce, "ina yi wa aminaina na kasar Sin godiya ainun, sabo da gudummowar da suke ta bayarwa ga wasannin motsa jiki, musamman kokarin da suka yi wajen gudanar da ayyukan shirya wasannin Olympic na Beijing. Tun daga yau, ya kasance da kwanaki da yawansu bai kai 1,000 ba kafin bude wasannin Olympic na Beijing, ina son kalubalance su da su ci gaba da yin kokari sosai wajen yin ayyukansu don shirya wasannin Olympic na Beijing da kyau kwarai. Ta haka birnin Beijing zai sami wani babban sakamako mai kyau sosai. Ina yi muku fatan alheri, na gode!" (Halilu)
|