Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 17:19:00    
Kasar Sin za ta zuba kudin Sin yuan miliyan 500 wajen kiyaye damshin kasa a bana

cri

Ran 9 ga wata, wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya sami labari daga hukummar gandun daji ta kasar Sin cewa, kasar Sin za ta zuba kudin Sin yuan mililyan 500 wajen kiyaye damshin kasa da kuma kafa shiyyoyin kiyaye halittu a cikin shekarar da muke ciki.

An ba da karin haske cewa, a cikin shekaru misalin 10 da suka wuce, fadin tabkoki ya ragu sosai a kasar Sin, tabkokin da yawansu ya kai fiye da kashi 70 cikin dari a kasar Sin suna fama da matsalar gurbacewa, sa'an nan kuma, ya zuwa yanzu ba a hana lalata damshin kasa da kuma lalacewar amfanin damshin kasa ba.

Wani jami'i ya bayyana cewa, bisa shirin da aka tsara kan aikin kiyaye damshin kasa na duk fadin kasar Sin a cikin shekaru 5 masu zuwa, an ce, kasar Sin za ta kara zuba kudi wajen kiyaye damshin kasa da kafa shiyya-shiyyar kiyaye halittu, tana fuskantar zarafin bukasuwa da ba safai a kan samu ba wajen kiyaye da mayar da ingancin yanayin damshin kasa.(Tasallah)