Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 16:59:40    
Matsayin kasar Sin a kan gwaje-gwajen makamai masu linzami da Koriya ta arewa ta yi

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun mai sauraronmu daga birnin Zaria na jihar Kaduna ta tarayyar Nijeriya, wato Sarki B. Zaria. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya yi mana tambaya cewa, mene ne matsayin kasar Sin dangane da gwaje-gwajen rokokin yakin da Koriya ta arewa ta yi a kwanan baya.

Kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na arewa maso gabashin Asiya matsayi ne da gwamnatin kasar Sin take dauka a kullum, kuma daga wannan matsayi ne, gwamnatin kasar Sin take fatan bangarori daban daban za su bi hanyar shawarwari da kuma yin kokari a fannin diplomasiyya, don daidaita batutuwan da ke da nasaba da zirin Koriya cikin lumana.

A ran 5 ga watan Yuli da ya gabata, kafar watsa labaru ta CNN ta bayar da labarin cewa, a ran nan da sassafe, Koriya ta arewa ta harba makamai uku masu linzami, ciki har da wani mai dogon zango irin na Taepodong-2, wanda kuma ba a yi nasarar harba shi ba.

Daga baya kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta arewa, ya tabbatar da cewa, Koriya ta arewa ta harba makamai masu linzami, amma wannan wani kashi ne na aikin inganta karfin tsaron kasar, wanda kuma ba shi da nasaba da shawarwarin bangarori shida dangane da batun nukiliyar zirin Koriya. Har zuwa yanzu dai, Koriya ta arewa ba ta canja niyyarta ta tabbatar da rashin kasancewar makaman nukiliya a zirin Koriya ta hanyar shawarwari ba.

A ran nan kuma, yayin da take amsa tambayoyin manema labaru dangane da gwaje-gwajen harba makami mai linzami da Koriya ta arewa ta yi, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Madam Jiang Yu ta ce, kasar Sin tana nuna kulawa sosai ga al'amarin, kuma tana fatan bangarori daban daban za su yi hakuri, kada dai su dauki matakan da za su kara tsananta halin da ake ciki. Ta ce, har kullum, kasar Sin tana taka rawa mai kyau a wajen sassauta halin da ake ciki a zirin Koriya da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, kuma kasar Sin za ta ci gaba da kokartawa a wajen sa kaimi ga shawarwarin da ke tsakanin bangarori shida da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya.

Madam Jiang ta kara da cewa, ainihin matsayin kasar Sin a kan harkokin zirin Koriya shi ne kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na shiyyar, kuma shawarwari wata hanya ce mai amfani a wajen daidaita matsaloli. Muna fatan za a sassauta halin da ake ciki a shiyyar bisa kokari a fannin diplomasiyya. Wannan ya dace da moriyar bangarori daban daban.

Yayin da aka tabo magana a kan shawarwarin gaggawa da kwamitin sulhu ya yi a ranar da ta wuce dangane da al'amarin. Madam Jiang ta ce, kasar Sin ta shiga shawarwarin da kwamitin sulhu ya shirya kamar yadda ya kamata. A ganinmu, ya kamata kwamitin sulhu ya mayar da martani kamar yadda ya kamata, a sa'i daya kuma, kamata ya yi kwamitin sulhu ya mayar da martanin da zai amfana wajen tabbatar da kwanciyar hankali a zirin Koriya da arewa maso gabashin Asiya, kuma zai taimaka wajen cimma nasara a kokarin diplomasiyya.

Bayan haka kuma, a ran 11 ga watan jiya, yayin da shugaban kasar Sin Hu Jintao ke ganawa da tawagar sada zumunta ta kasar Koriya ta arewa a birnin Beijing, ya ce, har kullum dai, kasar Sin tana dukufa a kan kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na zirin Koriya, kuma tana tsayawa tsayin daka a kan daidaita batutuwan da ke shafar zirin Koriya cikin lumana kuma ta hanyar shawarwari. Kasar Sin tana son yin kokari tare da bangarori daban daban, don sa kaimi ga shawarwarin da ke tsakanin bangarori shida da kuma kiyaye zaman lafiya na zirin Koriya da kuma yankunan arewa maso gabashin Asiya.

Kafin wannan kuma, kasar Sin ta bayar da wata daftarin sanarwar shugaba ga kwamitin sulhu dangane da gwaje-gwajen makamai masu linzami da Koriya ta arewa ta yi, inda ta yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su yi hakuri, kuma su yi shawarwari don neman samun wata hanyar da za ta daidaita batun cikin lumana kuma daga dukan fannoni. Ban da wannan, daftarin ya kuma yi kira ga bangarori daban daban da su yi kokari tare, don maido da shawarwarin da ke tsakanin bangarori shida tun da wuri.(Lubabatu Lei)