Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 16:34:05    
Shugaban Lebanon ya yi watsi da shirin jibge sojojin taron dangi a kudancin kasar

cri

Jiya Talata, shugaban kasar Lebanon Mr.Emile Lahoud ya furta, cewa bangaren Lebanon yana fatan za a kara yawan sojoji masu kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake Lebanon da kuma kara samar da makamai; A sa'I daya kuma Mr. Lahoud ya jaddada, cewa bangaren Lebanon ya yi watsi da shirin jigbe sojojin taron dangi a kudancin kasar kuma ba zai amince da ko wadanne sojojin da za a aiko bisa sunan Majalisar Dinkin Duniya amma ba tare da karbar jagoranci daga wajenta ba.

A wannan rana, Mr. Lahoud ya sake neman sojojin Isra'ila da su janye jikinsu zuwa bayan iyakar kasashen Lebanon da Isra'ila. Ya kuma kara da , cewa ba za a iya dakatar da rikicin da ake yi tsakanin Lebanon da Isra'ila ba idan ya kasance da sojojin Isra'ila a Lebanon. Bugu da kari kuma Mr. Lahoud ya yi Allah wadai da kasar Amurka saboda ta shagwaba Isra'ila a cikin rikicin da ake yi tsakanin Lebanon da Isra'ila; Dadin dadawa ya bayyana ra'ayinsa, cewa shirin kuduri na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda kasashen Amurka da Fransa suka kaddamar ba shi da gaskiya.

Daga nasa wajen, firaminista Ehud Olmert na Isra'ila ya furta, cewa yana mai sha'awar shawarar jibge sojojin gwamnatin Lebanon a kudancin kasar, wadda gwamnatin Lebanon ta gabatar.

A wata sabuwa kuma, an ce, ministan harkokin waje na kasar Fransa Mr.Phillippe Dauste-Blazy shi ma ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya sa ido kan wannan shawara. Ya kuma kara da, cewa wannan dai wani kudurin siyasa ne mafi muhimmanci, wanda kuma ya bayyana cewa bangarori daban daban na kasar Lebanon suna da burin goyon bayan gwamnatin kasar wajen aiwatar da ikon mulkin kai a fadin duk kasar. ( Sani Wang )