Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 17:10:44    
Ali Gedi yana sulhunta rikicin da ke gaban gwamnatin wucin gadi ta Somaliya

cri
A ran 8 ga wata, malam Ali Mohamed Gedi, firayin ministan gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya wanda ke daukar nauyin kafa wata wabuwar majalisar ministocin kasar da aka dora masa, ya kai ziyara ga dattijan kabilu iri iri wadanda suke da tasiri sosai a garin Baidoa domin neman goyon bayan kafuwar sabuwar majalisar ministocin gwamnatin. Ra'ayoyin jama'a suna ganin cewa, wannan ziyara tana daya daga cikin ayyukan da malam Gedi ya yi wajen yunkurin daidaita rikicin da ke gaban gwamnatin wucin gadi ta Somaliya.

Malam Abdirahman Mohamed Nur Dinari, kakakin gwamnatin wucin gadi ta Somaliya ya ce, a wannan rana, malam Gedi ya yi shawarwari da dattijai kan takardar sabbin membobin gwamnatin domin yunkurin kammala aikin kafa sabuwar majalisar ministoci a cikin mako 1. a ran 7 ga wata, lokacin da malam Abdullahi Yusuf Ahmed, shugaban wucin gadi na kasar Somaliya ya soke majalisar ministocin kasar, ya ce, za a rage yawan ministoci da mataimakansu a cikin sabuwar majalisar ministoci. Wato, a cikin tsohuwar gwamnatin wucin gadi, akwai ministoci 42 tare da mataimakansu 80. Amma bisa shirin da aka tsara, sabuwar majalisar ministocin gwamnatin wucin gadi za ta kunshi ministoci 31 tare da mataimakansu 44.

A shekarar 2004 ce aka kafa gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya da aka soke ta kwanan baya a birnin Nairobi na kasar Kenya. A watan Yuni na shekarar 2005, wannan gwamnatin wucin gadi ta koma kasarta, amma domin ba ta da karfi, kuma ba ta iya daukar kowane mataki, ba ta iya sarrafa halin da ake ciki a kasar Somaliya. Sakamakon haka, halin rashin kwanciyar hankali da ake ciki a kasar bai samu ainihin kyautatuwa ba. Har ma ba a iya tabbatar da tsaro ga wannan gwamnatin wucin gadi, wannan gwamnatin wucin gadi ta Somaliya ba ta iya shiga birnin Mogadishu, babban birnin kasar ba, sai dai tana tafiyar da harkokinta a garin Baidoa, inda ke kudu maso yamma da birnin Mogadishu da kilomita 250. Tun daga farkon shekarar da muke ciki, kungiyar kawancen kotunan addinin Musulunci, wato wata kungiya mai rike da makamai ta addinin Musulunci ta kasar Somaliya ta kara samun karfinta. Ta kan yi yaki sosai da dakarun madugun 'yan tawaye a birnin Mogadishu. A watan Yuni na shekarar da muke ciki, kungiyar kawancen kotunan addinin Musulunci ta mallaki birnin Mogadishu da yawancin wuraren kudancin kasar. Sakamakon haka, ta zama wata kungiya wadda ta fi karfi a Somaliya, kuma tana barazana ga gwamnatin wucin gadi ta Somaliya sosai.

Ko da yake gwamnatin wucin gadi ta Somaliya da kungiyar kawancen kotunan Musulunci sun riga sun rattaba hannu kan wata sanarwa a tsakanin watan Yuni, inda suka yarda da cewa za su daina dukkan matakan adawa da juna, kuma suka tsai da kudurin shirya sabon shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakaninsu tun daga tsakanin watan Yuli, amma, domin gwamnatin wucin gadi ta Somaliya ta kai suka kan kungiyar kawancen kotunan Musulunci cewa wannan kungiyar kawance yana kisan gillar fararen hula da magoyan gwamnatin wucin gadi. Sannan kuma, gwamnatin wucin gadi tana ganin cewa, kungiyar kawancen kotunan Musulunci ta samu goyon baya daga kungiyoyin nuna ta'addanci na kasashen waje. Sabo da haka, gwamnatin wucin gadi ta tsai da kudurin cewa, ba za ta ci gaba da yin shawarwari da wannan kunigya ba. Sakamakon haka, nan da nan ne dakarun kungiyar kawancen kotunan Musulunci sun taru a wuraren da ke wajen Baidoa. Babu sauran hanyar da za ta iya zaba, sai gwamnatin wucin gadi ta Somaliya ta roki kasar Habasha da ta tura sojojinta domin kiyaye ta. A sakamakon haka, wannan gwamnatin wucin gadi da aka kafa ta yau da shekara 1 da ta wuce kawai ta sake shiga cikin mawuyacin hali.

A waje daya kuma, domin ya kasance da ra'ayoyi daban kan matsayin da ake bi game da sojojin kasashen waje da batun yadda za a yi shawarwarin neman zaman lafiya a tsakanin gwamnati da kungiyoyin da ke rike da makamai na addinai, an haddasa tashin hankali a cikin gwamnatin wucin gadi ta Somaliya. Tun daga karshen kwanaki 10 na watan Yuli, muhimman jami'i a kalla 43 na gwamnatin sun yi murabus daga mukamansu domin nuna bakin ciki saboda gwamnatin ba za ta dauki matakai masu karfi ba wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar. Har ma wasu 'yan majalisar dokokin kasar sun gabatar da shirin rashin amincewa da Ali Mohamed Gedi, inda ake son koren Gedi daga mukaminsa. Ko da yake ba a amince da wannan shiri ba a zauren majalisar ba, malam Gedi ya ci nasarar ci gaba da zauna a kan mukaminsa, amma, wannan wani babban burga ne ga gwamnatin wucin gadi.

Yanzu, an fi mai da hankali kan malam Gedi. Za a ga yaya zai kafa wata sabuwar majalisar ministocin gwamnati da kowane bangare zai amince da ita, ko yaya zai iya janye gwamnatin wucin gadi daga mawuyacin hali. Manazarta suna ganin cewa, wannan ba abu mai sauki ba ne, wata jarrabawa ce mai tsanani ga karfinsa na mulkin kasar. (Sanusi Chen)