Kungiyar wasan kwallon kafa na mata na kasar Sin ta kawo wa masu sha'awar kwallon wani abun al'ajabi ba zato ba tsammani, wato ke nan ta nuna rawar gani har ta zama zakara a gun gasar cin kofin Asiya ta 15 ta wasan kwallon kafa na mata da aka kawo karshenta a ran 30 ga watan jiya. Hakan ya himmantar da 'yan wasan wajen sake samun aniya a gun wasa.
Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin wadda ta taba samun lambar azurfa a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics da aka yi a Atlanta na kasar Amurka da kuma lambar azurfa a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 1999 ta taba samun matsayin gaba a Asiya har a duk duniya; Amma 'yan wasan kungiyar ba su taba samun lambar zinariya a gun irin wannan gasa ba bayan da suka samu lambar zinariya har sau bakwai a jere a gun gasar cin kofin Asiya a shekarar 1999. Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ba ma kawai ta rasa matsayin ci gaba a duniya ba, har ma ta yi kasa-kasa a gasannin da aka yi tsakanin kasashen Asiya; Alal misali: ta sha kaye har sau bakwai daga hannun 'yan wasan kwallon kafa na Korea ta Arewa, kuma ta sha kaye sosai daga hannun 'yan wasan kasar Jamus da ci 8 da nema.
Lallai kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta bakanta ran masu sha'awar kwallon na kasar Sin.
Amma bisa wannan hali dai, kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta zama zakara a gun gasar cin kofin duniya da aka yi a wannan shekara. ' yar wasa mabugin gaba mai suna Han Duan ta furta, cewa: ' Nasarar da muka samu a wannan gami ta sake kara aniyarmu da kuma faranta ran masu sha'awar kwallo. Idan mun kasa samun lambar zinariya a gun gasar cin kofin Asiya da aka yi a wannan gami, to labuddah hakan zai zama tamkar bugun tsiya ne muka sha a cikin zukatanmu, kuma babu tantama za a yi shakkar cewa ko kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana da kyakkyawar makoma a nan gaba? Na yi imanin cewa kungiyarmu za ta iya samun ci gaba cikin taka tsan-tsan a shekarar 2007 da shekarar 2008'.
Kyakkyawan sakamakon da 'yan kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin suka samu a gun gasar cin kofin Asiya da aka yi a wannan gami ba wai lambar zinariya ta farko kawai da suka samu tun shekaru 7 da suka shiga ba, har ma karfin zuciya ne suka nuna a duk tsawon lokacin gasar neman daukar kofin. Ana sane da, cewa a farkon gasar da aka yi tsakanin kananan kungiya, sakamakon da suka samu bai kai a zo a gani ba, har sun sha kashi daga hannun 'yan wasan kasar Japan wadda take bayanta cikin dogon lokaci. Amma, daga wannan lokaci ne dukan 'yan wasan kasar Sin suka yi fintinkau a gun gasar har sun lallasa 'yan wasan kungiyar Korea ta Arewa; Dadin dadawa, sun lashe 'yan wasan kasar Australiya wadda take daukar nauyin bakuncin 'yan wasa a wannan gami da ci shida da hudu ta hanyar buga finalite wato bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Ban da wannan kuma, an yi farin ciki da gano wata 'yar wasa tauraruwa mai suna Ma Xiaoxu mai shekaru 18 da haihuwa dake cikin kungiyar kasar Sin. An daukaka wannan yarinya da sunan ' yar wasan gaba mafi kwazo' a wannan gasa. Lallai Ma Xiaoxu ta cancanci samun wannan lamba mai daraja saboda ta nuna rawar gani a dukkan gasanni musamman ma gasar kusa da karshe da kuma gasar karshe da aka gudanar. Ma Xiaoxu ta fadi, cewa: ' Makasudin nan gaba shi ne halartar taron wasannin motsa jiki na Asiya da kuma sauran gagaruman gasanni da za a yi a shekarar 2007 da kuma shekarar 2008'.
Babban mai koyar da 'yan wasa mata na kasar Sin Mr. Ma Liangxing ya yi farin ciki da hangen nesa, cewa: ' Da ni, da kungiyar wasan, da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar da kuma masu sha'awar kwallon dukansu ba za su gamsu da samun lambar zinariya a gun gasar cin kofin Asiya kawai ba. ( Sani Wang )
|