Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-09 10:01:22    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (03/08-09/08)

cri

Yau ran 8 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru biyu da suka yi saura don shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. Kwanakin baya ba da dadewa ba, shugaban kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing Mr. Liu Qi ya karbi ziyarar da muhimman kafofin watsa labaru na kasar Sin suka yi masa, inda ya furta, cewa tun shekaru biyar da suka shige bayan da aka soma share fage ga taron wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008, kwamitin shirya taro wasannin na Beijing ya tabbatar da dukkan manufofi iri daban daban cikin daidai lokaci, wadanda ya tsara a da. Hakan ya aza tushe mai inganci ga gudanar da wani taron wasannin motsa jiki na Olympics dake da sigar musamman kuma bisa matsayin koli. Mr. Liu Qi ya kara da,cewa bisa babban goyon baya daga gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da sa hannu cikin himma da kwazo da mutanen duk kasar da Sinawa 'yan kaka-gida ,da Sinawa mazauna kasashen ketare da kuma aminai na kasa da kasa suka yi, ana gudanar da ayyukan gina filaye da dakunan wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing lami-lafiya ; kuma ana yin aikin share fage ga taron wasannin motsa jiki na Olympics na nakasassu kamar yadda ya kamata ; bugu da kari kuma an samu kyakkyawan sakamako a fannin raya kasuwanni, da yin farfaganda da kuma yada al'adun wasannin Olympics.

A albarkacin zagayowar ranar cika shekaru biyu da suka rage domin gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008, jiya Litinin, a nan Beijing, kwamitin shirya taron wasannin na Beijing ya kaddamar da zanen wasanni iri iri na Olympics na Beijing a shekarar 2008. An zana zane-zane guda 35, wadanda suka siffanta wasanni iri 35 kamar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ,da wasan tseren kwale-kwale, da wasan badminton da kuma wasan kundunbala da lankwashe-lankwashe wato Gymnastics da dai sauransu. Za a yi amfani da wadannan zane-zane ne a fannin tsarin ba da jagoranci ga bin hanyoyin mota na taron wasannin Olympics, da talla, da kayatar da muhalli, da watsa labaru ta T.V. da kuma na yin fasalin abubuwan tunawa da taron wasannin.

A ran 3 ga watan da muke ciki, hadaddiyar kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa ta shelanta, cewa a hukunce ne aka tabbatar da matsayin bajinta na duniya da shahararren dan wasa mai suna Liu Xiang na kasar Sin ya kago a gun wasan gudun tsallake shinge na tsawon mita 110 na maza da dakika 12 da digo 88.

A kwanakin baya ba da dadewa ba, hadaddiyar kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa ta tabbatar da, cewa akwai kungiyoyi daga kasashe da jihohi da yawansu ya kai 182 da za su halarci gasar cin kofin duniya ta 11 ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle na matasa da za a gudanar daga ran 15 zuwa ran 20 ga watan nan a nan Beijing. ( Sani Wang )