Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 16:55:15    
Mutane sun kara jin dadin ganin sabbin ni'imtattun wurare na Sanxia na kogin Yangtse

cri

Sabo da an gama gina madatsar ruwa ta Sanxia, matsayin zurfin ruwa na Sanxia na kogin Yangtse ya karu zuwa mita 135, ta yadda an samar da sabbin ni'imtattun wuraren Sanxia na kogin Yangtse, wanda shi ne kwazazabo kurum da ake iya ziyararsa a cikin jiragen ruwa tun daga farko har zuwa karshe. A cikin bayanin musamman da za mu ci gaba da karanta muku, za mu dan gutsura muku wadannan sabbin ni'imtattun wurare.

Mataimakin shugaban hukumar yawon shakatawa ta birnin Yichang na lardin Hubei na kasar Sin Mr. Gao Chao ya bayyana cewa, bayan da matsayin zurfin ruwa na Sanxia na kogin Yangtse ya kai mita 135 a watan Yuni na shekarar da muke ciki, a galibi dai ruwan bai hadiye manyan wuraren shakatawa da ke cikin Sanxia na kogin Yangtse ba, a maimakon haka, an samu sabbin ni'imtattun wurare da yawa. Yanzu ma iya cewa, Sanxia na kogin Yangtse ya kara samun kyaun gani. Ya ce,

'da can, Sanxia na kogin Yangtse ya yi suna ne saboda girmansa. Amma bayan da aka fara tattara ruwa a cikin madatsar ruwa ta Sanxia, ruwa ya fara tafiya sannu sannu, kuma ya fara zama mai tsabta, an fara jin dadin ganin manyan duwatsu da ke gabobin kogin Yangtse da kuma tafik mai kyaun gani. Ma iya cewa, tsoffin wuraren shakatawa na Sanxia na kogin Yangtse sun ci gaba da nuna kyaun gani nasu, a sa'i daya kuma, sabbin ni'imtattun wurare da aka samu a nan sun soma jawo hankulan mutane.'

A cikin Sanxia na kogin Yangtse akwai wani rafi mai suna Shennong, wanda ya shahara ne a gida da kuma waje. Tsawonsa ya kai kilomita 60, akwai hayi masu tsawo a gabobinsa, inuwar manyan duwatsu da kwarran gorori sun fito a saman ruwa, ta haka ruwan ya kara zama kore. Lokacin da masu yawon shakatawa suke yin shakawata cikin kwale-kwale a nan, sai ka ce, kore ya kewaye su. Iska tana da dadi, kuma ana shiru a nan babu kara, tsuntsaye sun yi kuka lokaci-lokaci, wani lokaci kuma, masu aiki cikin kwalekwale sun rera wakoki, shi ya sa masu yawon shakatawa sun ji sun nisantar da kansu daga duniyarmu mai yawan hayaniya.

Mai ja-gorar masu yawon shakatawa madam Wang Yuan ta ba da karin haske cewa, a zahiri kuma, a da, kwalekwale ba su iya shiga cikin rafuka kamar rafin Shennong sosai ba, saboda ruwan ba ya da zurfi. Amma bayan da aka tattara ruwa a cikin madatsar ruwa ta Sanxia, kwalekwale su kan iya shiga cikin wadannan rafuka, masu yawon shakatawa sun iya jin dadin ganin ni'imtattun wurare a nan. Ta kuma kiyasta cewa, yin shakatawa cikin kwalekwale a cikin rafuka zai jawo hankulan masu yawon shakatawa da suka ziyarci Sanxia na kogin Yangtse.

A zahiri kuma, saboda an fara gina madatsar ruwa ta Sanxia tun daga shekaru 90 na karnin da ya gabata, Sanxia na kogin Yangtse ya fara shahara a duk duniya, masu yawon shakatawa na kasashen waje sun kai ziyara a nan daya bayan daya. Sanxia na kogin Yangtse ya zama muhimmin wuri ne da masu yawon shakatawa na kasashen waje suka kai ziyara.

Mr. Huang Jie, wanda ke aiki a cikin sashen harkokin zirga-zirga na babban ofishin harkar yawon shakatawa na kasa da kasa na kasar Sin wato China International Travel Service, ya yi bayanin cewa, saboda karuwar matsayin zurfin ruwa na Sanxia na kogin Yangtse, shi ya sa, masu yawon shakatawa na kasashen waje suka kara son yin ziyara a nan a lokacin zafi. Ya ce,

'mun samar wa masu yawon shakatawa na kasashen waje da hidimar yawon shakatawa mai gajeren zango, wato kaiwa da kawowa tsakanin birnin Chongqing de birnin Yichang na lardin Hubei. A galibi dai, sun yi haya jiragen ruwa. Wuraren shakatawa da ke gabobin kogin Yangtse su ma sun jawon hankulan masu yawon shakatawa na kasashen waje, suna da kyaun gani sosai.'

Yanzu an shiga mataki na farko wajen tattara ruwa a cikin madatsar ruwa ta Sanxia. Bayan da aka kammala aikin madatsar ruwa ta Sanxia duka a shekarar 2009 mai zuwa, matsayin zurfin ruwa na Sanxia na kogin Yangtse zai kai mita 175, a lokacin nan, ni'imtattun wurare na Sanxia na kogin Yangtse zai kara faranta wa mutane rayuka.

Mataimakin shugaban Gao Chao yana ganin cewa, bayan da aka gama aikin madatsar ruwa ta Sanxia duka, masu yawon shakatawa na gida da na waje za su kara jin dadin ganin ni'imtattun wurare na halitta da manyan duwatsu da babban tabki da kuma koren ruwa.(Tasallah)