Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-08 15:48:16    
Tilas ne a je wajen likta idan rashin barci ya ba da tasiri kan harkokin yau da kullun

cri

Kusan dukan mutane sun taba fama da rashin barci, a cikinsu wane ne suke bukatar zuwa asibiti? Masana masu ilmin likitanci sun tuna wa mutane da cewa, masu fama da rashin barci wadanda rashin barci ya riga ya ba da tasiri kan harkokin yau da kullun ya kamata su je wajen likitocin musamman cikin lokaci, sa'an nan kuma, su sha magunguna yadda ya kamata. Yanzu mutanen kasar Sin ba su amince da dora muhimmanci kan rashin barci sosai ba. 'Rahoton bincike kan halin da mutane na birane 6 na kasar Sin suke ciki a fannin rashin barci a shekarar 2006' ya nuna cewa, masu fama da rashin barci da yawansu ya kai kashi 87 cikin dari ba su taba zuwa asibiti ba, yawancin masu fama da rashin barci da suka taba zuwa asibiti ba su je wajen likitocin musamman ba; masu fama da rashin barci da yawansu ya kai kashi 73 cikin dari ba su taba shan magunguna ko kuma kuma daukan sauran matakai don kyautata barci ba.

Zaunannen wakilin na kwamitin sashen duba masu motsowar kwakwalwa na hadaddiyar kungiyar ilmin likitanci ta kasar Sin shehun malami Li Shunwei ya yi nuni da cewa, rashin barci cikin dogon lokaci ba ma kawai ya ba da tasiri kan zaman rayuwa da ayyukan yau da kullun ba, har ma ya kawo wa lafiyar mutane illa. Don haka, masu fama da rashin barci, musamman ma wadanda rashin barci ya riga ya ba da tasiri kan harkokin yau da kullun, ya kamata su je asibiti cikin lokaci, don neman samun taimako daga wajen likitoci na musamman.

Shehun malami Fan Dongsheng, mataimakin shugaban asibiti na uku na jami'ar Beijing kuma darektan sashen duba masu motsuwar kwakwalwa ya nuna cewa, wasu masu ciwon da ba su son shan magani suna ganin cewa, za a dogara da magunguna domin shan magunguna, za a ba da tasiri maras kyau kan jikunansu. Wannan ba daidai sosai ba ne. Yin jiyya bisa bukata da kuma shan dan magungunan barci kadan lokaci-lokaci sun iya kyautata ingancin barci, a sa'i daya kuma, ana kokarin rage tasiri maras kyau.(Tasallah)