Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 20:37:01    
Sabunta: Lebanon ta nemi kwamitin sulhu na M.D.D. da ya gyara shirin kudurin da kasashen Amurka da Faransa suka gabatar

cri
A ran 6 ga wata, kasar Lebanon ta bayar da sanarwa, inda ta nemi kwamitin sulhu na M.D.D. da ya gyara shirin kudurin da kasashen Amurka da Faransa suka gabatar domin kara wasu sharuda ciki har da sharadin janye jikin sojojin Isra'ila daga kasar Lebanon. A sa'i daya kuma, kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da kasar Isra'ila suna ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu.

A wannan rana, kungiyar wakilan kasar Lebanon da ke M.D.D. ta gabatarda ra'ayoyin gyara wannan shirin kuduri ga rukunin kwararru na kwamitin sulhu na M.D.D. Bisa ra'ayoyin da bangaren Lebanon ya gabatar, bangaren Lebanon ya nemi Isra'ila da ta mika wa sojoin M.D.D. wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon wuraren yaki da suke cikin hannun sojojin Isra'ila yanzu lokacin da ake kawo karshen wutar yaki. Sannan kuma, ya kamata sojojin Isra'ila su janye jikinsu sai iyakar kasa ta launin shudi. Daga baya, ya kamata sojojn M.D.D. da ke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon su mika wa sojojin gwamnatin Lebanon ikon mallakar yankunan sassautuwa da ke kudancin Lebanon a cikin sa'o'i 72.

A sa'i daya kuma, kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da kasar Isra'ila suna ci gaba da yin fada da makamai a tsakaninsu. Hare-haren da jiragen sama na yaki na kasar Isra'ila suka kai wa kudancin kasar Lebanon a ran 7 ga wata da sassafe sun zama sanadiyar mutuwar fararen hula a kalla 11. Ban da wannan kuma, jiragen sama na yaki na kasar Isra'ila sun kai hare-haren bama-bamai ga wasu muhimman wurare da ke gabashin kasar Lebanon a ran nan. Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta sake harbar rokoki ga birnin Haifa na kasar Isra'ila, inda mutane a kalla 3 suka mutu, yayin da gomai suka jikata.(Tasallah)