Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 18:23:56    
Za a yi taron musamman na ministocin harkokin wajen kawancen kasashen Larabawa a birnin Beirut

cri
A ranar 7 ga wata, za a yi taron musamman na ministocin harkokin wajen kawancen kasashen Larabawa a birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, inda mahalartan taron za su tattauna yadda za a kawo karshen babban rikicin da ke tsakanin kungiyar Hezbollah da Isra'ila tun da wuri.

Wani jami'in gwamnatin Lebanon ya fayyace a ranar cewa, mahalartan taron za su bayyana goyon bayansu ga shirye-shirye bakwai da firaministan Lebanon, Fuad Siniora ya gabatar dangane da daidaita rikicin da ke tsakanin kasarsa da Isra'ila, ciki har da Isra'ila ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon da kuma inganta aikin MDD na kiyaye zaman lafiya a kudancin Lebanon da kuma jibge sojojin gwamnatin Lebanon a yankin Lebanon da ke kan iyakar da ke tsakanin Lebanon da Isra'ila da kuma kwance damarar dakarun kungiyar Hezbollah da dai sauransu.(Lubabatu Lei)