Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 15:53:26    
Shugabannin makarantun firamare da sakandare na kasar Amurka sun zo kasar Sin don fahimtar al'adun Sinanci

cri

Al'adun gargajiya na kasar Sin suna da dogon tarihi, kuma ko a kasar Sin ko a kasashen waje, mutane marasa lissaftuwa suna nuna sha'awa sosai gare su. Bisa matsayinsa na wata alama ce ta al'adun gargajiya na kasar Sin, Sinanci wani harshe ne mai dogon tarihi. Yanzu mutanen kasashen waje masu yawa suna son koyon Sinanci, ta yadda za su fahimci al'adun gargajiya na kasar Sin.

Yanzu a kasar Amurka, mutane da yawa suna koyon Sinanci. Bisa wani binciken da kwamitin kula da harkokin jami'o'in Amurka ya yi, an ce, makarantun firamare da sakandare kusan 2500 na Amurka suna son koyar da Sinanci, kuma a ran 1 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, shugabannin makarantun da suka zo daga wadannan makarantu sun kawo wa kasar Sin ziyara. Mataimakin shugaban ofishin harkokin yada Sinanci zuwa kasashen waje na kasar Sin Ma Jianfei ya bayyana cewa,

"Yanzu makarantun firamare da sakandare 2500 na kasar Amurka suna son koyar da Sinanaci, amma a hakika dai, aiwatar da batun ba abu mai sauki ba. Da ma shugabannin makarantun firamare da sakandare da kuma malamai masu sa ido ga ayyukan koyar da harsunan waje na kasar Amurka ba su san kasar Sin sosai ba, shi ya sa ba su san yadda ya kamata a koyar da Sinanci ba. Yanzu sun zo kasar Sin, sun ga wasu albarkatun da muka shirya musu, kamar malamai da littattafan koyarwa, kuma su kansu ne suka fahimci al'adun gargajiya na kasar Sin, dukkan wadannan abubuwa za su karfafa zuciyarsu sosai wajen aiwatar da ayyukan koyar da Sinanci bayan da suka koma gida."

E, haka ne, wannan kuwa nufinsu ne da shugabannnin makarantun firamare da sakandare na Amurka suka yi wannan ziyara a kasar Sin. Shugaban makarantar sakandare na birnin Harbor na jihar Maryland ta kasar Amurka Albert Thompson ya bayyana cewa,

"dalilin da ya sa na kawo wa kasar Sin ziyara shi ne sabo da ina son fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin, kuma bayan da na koma gida, zan yi wa dalibai bayani kan ziyarar, ta yadda za su nuna sha'awa kan koyon Sinanci a kasar Sin da kuma fahimtar duniya."

Shugabannin makarantu da jami'ai masu kula da ayyukan koyarwa na kasar Amurka sun ziyarci fadar bazara da titunan Beijing wanda ake kiransu Hutong da sauran wuraren yawon shakatawa masu sigar mumsamman na kasar Sin. Xu Jialu, mataimakin shugaban majalisar dokoki ta kasar Sin kuma shahararren masani a fannin harsuna ya ba da lacca ga bakin Amurka kan al'adun Sinanci, ta yadda za a karfafa fahimtarsu kan al'adun gargajiya na kasar Sin.

Ban da wannan kuma, sun ziyarci makarantun firamare da sakandare na birnin Beijing, kuma sun yi mu'amala tare da malamai da dalibai don san yadda a kan yi ayyukan koyarwa a kasar Sin da kuma yadda ya kamata a koyar da Sinanci ga dalibai masu dalibta.

Ko da yake shugabannin makarantu da jami'ai masu kula da ayyukan koyarwa na Amurka sun kawo wa kasar Sin ziyara a mako guda kawai, amma al'adun gargajiya na kasar Sin da kuma bunkasuwar kasar Sin cikin saurin sun shaku cikin zuciyarsu sosai. Kuma suna ganin cewa, Sinanci zai fi karbuwa a ko ina a nan gaba. Madam Deborah Delisle, wata jami'a mai kula da ayyukan koyarwa ta birnin Heights na jihar Ohio ta kasar Amurka ta bayyana cewa,

"kasar Sin tana takawa muhimmiyar rawa a fannonin tattalin arziki da kuma al'adu a duk duniya. Kuma a duniya na nan gaba, dole ne a ji ra'ayoyi na sauran mutane, musamman ma ra'ayoyin Sinawa."

Bisa labarin da muka samu, an ce, ziyarar da shugabannin makarantun kasar Amurka suka yi a kasar Sin wani kashi ne na cudanyar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka kan al'adun harsuna, kuma bisa yarjejeniyar da ofishin kula da harkokin yada Sinanci zuwa kasashen waje na kasar Sin da kwamitin kula da harkokin jami'o'in Amurka suka daddale, za a shirya irin wannan ziyara sau da yawa a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ban da wannan kuma, ofishin kula da harkokin yada Sinanci zuwa kasashe waje na Sin zai tura mutane masu sai kai 50 zuwa kasar Amurka domin koyar da Sinanci a cikin shekaru uku masu zuwa, da samar da kudin karatu ga daliban Amurka nagari domin su zo kasar Sin kara ilminsu, da kuma horar da malamai masu koyar da Sinanci a Amurka, ta yadda za a nuna goyon baya ga makarantun Amurka wajen ayyukan koyar da Sinanci.(Kande Gao)