Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 15:46:03    
Kabilar Rasha

cri

Da farko dai za mu bayyana muku wata karamar kabila, wato kabilar Rasha. Sannan kuma, bari mu dandana wasu sannanun abincin kabilar Koriya. Yanzu ga bayani game da kabilar Rasha.

Mutanen kabilar Rasha wadanda suke da zama a nan kasar Sin jikokin Rasha ne. Yawancinsu suna da zama a birnin Yili da garin Tacheng da garin Aletai da birnin Urumqi na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. A shekarar 2002, lokacin da ake kidaya yawan mutanen kasar Sin, an samu adadi cewa, yawan mutane kabilar Rasha da ke da zama a nan kasar Sin ya kai dubu 15 da dar6 da 9. Dukkansu sun iya harshen Rasha.

Domin ba da dadewa ba ne mutanen kabilar Rasha suka zo suka yi zama a kasar Sin, mutane da yawa daga cikinsu suna da iyalai a Tarayyar kasashen Soviet. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an maido da dangantaka a tsakaninsu. Mutane da yawa sun nemi da a yarda da su koma garinsu. A shekaru 50 na karnin da ya gabata, bayan da gwamnatocin kasar Sin da Tarayyar kasashen Soviet suka tattauna kan batu, sun samu iznin koma garinsu a Tarayyar kasashen Soviet. Bugu da kari kuma, wasu mutanen kabilar Rasha da suka yi zama a kasar Sin sun je kasar Australiya da kasar Canada domin suna da iyalai a wadannan kasashe. Sabo da haka, yanzu, yawan mutanen kabilar Rasha da suke da zama a nan kasar Sin ya yi kadan.

A da, mutanen kabilar Rasha wadanda suka yi zama a garuruwa sun yi sana'o'in sarrafawa da sufuri da sana'ar hannu. Wasu kuma sun yi aikin gona. Mutanen kabilar Rasha da suka yi zama a kauyuka sun sari gonaki domin noman shuke-shuke. Wasu sun kiwon dabbobi. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, mutanen kabilar Rasha sun samu ikon dimokuradiyya kamar yadda sauran kabilun kasar Sin suka samu. Yawancinsu sun samu aikin yi. Wasu suna aiki a kamfanonin zirga-zirga da na tattalin arziki ko a cikin masana'antu, wasu suna aiki a cikin asibitoci. Sabo da haka, zaman rayuwarsu ya samu kyautatuwa sosai.

Jama'a masu sauraro, kowa ya sani, adabin Rasha yana da muhimmanci sosai a cikin al'adun duk duniya. Jikokin Rasha sun gado adabin baki da wakokin yara da karin magana da yawa daga kakani-kakaninsu.

Al'adar zaman rayuwar kabilar Rasha ta kasar Sin tana kama da ta kasar Rasha. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Rasha sun fi son gina gidaje da katako da dabo. Sun sa karan alkama a kan rufin wani gida. Mutanen kabilar Rasha suna son dasa itatuwa da ciyayi a wuraren da ke kewayan gida.

Haka nan kuma, muhimman abinci da mutanen kabilar Rasha suke ci shi ne burodi da waina iri iri. Kuma suna son cin kukumba da tumatir. Mijin kabilar Rasha suna son shan giya iri iri.

Samarin kabilar Rasha sun iya neman aure da kansu, amma, kafin a yi aure, dole ne su nemi amincewa daga iyayensu. An yarda da samarin kabilar Rasha su yi aure da samarin sauran kabilu.

Bugu da kari kuma, kabilar Rasha tana da biyayya da da'a. Lokacin da ake ganawa da juna, dole ne an gai da juna.(Sanusi Chen)