A ran 6 ga wata, kasar Lebanon ta bayar da sanarwa, inda ta nemi kwamitin sulhu na M.D.D. da ya gyara shirin kudurin da kasashen Amurka da Faransa suka gabatar domin kara wasu sharuda ciki har da sharadin janye jikin sojojin Isra'ila daga kasar Lebanon.
A wannan rana, kungiyar wakilan kasar Lebanon da ke M.D.D. ta gabatarda ra'ayoyin gyara wannan shirin kuduri ga rukunin kwararru na kwamitin sulhu na M.D.D. Bisa ra'ayoyin da bangaren Lebanon ya gabatar, bangaren Lebanon ya nemi Isra'ila da ta mika wa sojoin M.D.D. wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon wuraren yaki da suke cikin hannun sojojin Isra'ila yanzu lokacin da ake kawo karshen wutar yaki. Sannan kuma, ya kamata sojojin Isra'ila su janye jikinsu sai iyakar kasa ta launin shudi. Daga baya, ya kamata sojojn M.D.D. da ke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon su mika wa sojojin gwamnatin Lebanon ikon mallakar yankunan sassautuwa da ke kudancin Lebanon a cikin sa'o'i 72.
Ko da yake, bangaren Isra'ila bai bayyana ra'ayinsa game da wannan shirin kuduri ba, amma, Haim Ramon, ministan shari'a na gwamnatin Isra'ila ya fadi a ran 6 ga wata cewa, Isra'ila za ta iya amfana daga wannan shirin kuduri.
A sa'i daya kuma, malam Abdul Rahman al-Attiya, babban sakataren kwamitin neman hadin guiwar kasashen da ke bakin Gulf ya bayar da wata sanarwa a birnin Riyad, babban birnin kasar Saudi Arabiya a ran 6 ga wata, inda ya ce, dole ne kudarin kwamitin sulhu na M.D.D. game da rikicin da ake yi a tsakanin Isra'ila da Lebanon ya kunshi sharudan kawo karshen wutar yaki nan da nan da Isra'ila ta janye sojojinta daga yankunan Lebanon kwata kwata sai yankunan iyakar kasa ta launin shudi.
A waje daya kuma, Amr Moussa, babban sakataren Tarayyar kasashen Larabawa ya kai suka kan wannan shirin kudurin cewa, an yi kira ne da a daina kai wa juna hare hare kawai, amma ba a shafi batun kawo karshen wutar yaki nan da nan a cikin wannan shirin kuduri ba. (Sanusi Chen)
|