Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-07 10:53:34    
Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan matsalar jikata sojojin kasar Sin da ke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon

cri
A ran 6 ga wata a birnin New York, hedkwatar M.D.D., Mr. Liu Zhengmin, mataimakin wakilin kasar Sin da ke M.D.D. ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta nuna bakin ciki, kuma tana mai da hankali kan matsalar jikata sojojin kasar Sin 3 wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon.

Liu Zhengmin ya ce, wadannan sojoji 3 wadanda suke sansanin wucin gadi na M.D.D. da ke kudancin kasar Lebanon sun ji raunuka, matsala ce da ke nuna bakin ciki sosai. Gwamnatin kasar Sin ta riga ta nemi bangaren da abin ya shafa da ya samar musu aikin jiyya da ya wajaba cikin lokaci. Sannan kuma, bisa umurnin da gwamnatin kasar Sin ta nuna mata ne, kungiyar wakilan kasar Sin da ke M.D.D. ta kuma yi shawarwari da bangarorin Isra'ila da Lebanon wadanda suke yaki da juna. Bugu da kari kuma, ta yi shawarwari cikin gaggawa da Jean Marie Guehenno, mataimakin babban sakataren M.D.D. wanda ke kula da harkokin shimfida zaman lafiya, inda aka yi shawarwari cikin hali mai tsanani, kuma aka nemi M.D.D. da ta dauki dukkan matakan da suka wajaba domin tabbatar da lafiyar dukkan sojojin M.D.D. ciki har da sojojin kasar Sin wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon, kuma magance sake aukuwar irin wadannan matsaloli. Mr. Guehenno ya dauki alkawarin cewa, zai yi namijin kokari kuma za a dauki matakai domin tabbatar da lafiyar sojojin tabbatar da zaman lafiya.

Bugu da kari kuma, a wannan rana, Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin ya bayar da wani jawabi kan matsalar jikata sojojin kasar Sin 3 wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon, inda ya ce, bangaren kasar Sin ya riga ya yi shawarwari cikin hali mai tsanani da bangarorin Isra'ila da Lebanon wadanda suke yaki da juna kan wannan matsala. Ya kuma neme su da su dauki dukkan hakikanan matakai domin tabbatar da lafiyar sojoijn M.D.D. wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a Lebanon. Sannan kuma, bangaren kasar Sin ya nemi bangarorin biyu da suke yaki da juna da su kawo karshen wutar yaki a tsakaninsu nan da nan, kuma su koma hanyar neman daidaituwar matsalolin da ke kasancewa a tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari da hanyar siyasa. (Sanusi Chen)