Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-04 20:31:20    
Kayayyakin agaji da kasar Sin ta samar ga kasar Lebanon sun isa birnin Beirut

cri

A ran 4 ga wata da safe, kayayyakin agaji na jin kai na rukuni na farko da gwamnatin kasar Sin ta samar ga kasar Lebanon sun isa filin jirgin sama da ke birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon.

Wadannan kayayyakin da nauyinsu ya kai ton 40 suna kunshe ne da magunguna da na'urorin likita da injunan samar da wutar lantarki da tantuna da kuma barguna da dai sauransu. Ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Lebanon ya mika kayayyakin ga wakilan bangaren Lebanon a filin jiragen sama. Kuma bangaren Lebanon ya nuna godiya ga jama'ar kasar Sin da su samar da taimako ga shi lokacin da take fuskantar mawuyacin halin.(Kande Gao)