Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-04 17:03:59    
Kasar Sin tana kokarin raya sana'ar samar da kayayyakin gine-gine masu tsimin makamashin halittu

cri

Yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana ta samun bunkasuwa mai dorewa cikin sauri. Bisa sabuwar kididdigar da aka yi, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai fiye da kashi 10 cikin kashi dari a cikin farkon watanni 3 na shekarar da muke ciki. Sakamakon haka, halin da ake ciki a birane da kauyuka na kasar Sin ma yana samun sauye-sauye, sabbin gine-gine suna bulla a kullum. Sabo da haka, kasar Sin tana kokarin yin amfani da kayayyakin da suke tsimin makamashin halittu sosai.

Yanzu yawan fadin gine-ginen da aka yi a nan kasar Sin ya kai murabba'in mita a tsakanin biliyan 1.5 zuwa biliyan 2 a kowace shekara. An yi hasashen cewa, ya zuwa shekara ta 2020, fadin sabbin gine-ginen da za a gina zai kai murabba'in mita biliyan 30. Sabo da haka, idan ba a mai da hankali kan yunkurin tsimin yin amfani da makamashin halittu a kan sabbin gine-gine, nan da shekaru 20 masu zuwa ba, yawan makamashin halittu da za a yi amfani da su zai kai kashi 50 cikin kashi dari bisa na dukkan makamashin halittu da duk zaman al'ummar za ta bata.

A kwanan baya, Mr. Wang Guangtao, ministan kula da harkokin gine-gine na kasar Sin ya ce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta sa shirin tsimin makamashin halittu a kan gine-gine a cikin babban shirin raya kasar. " A cikin "tsarin raya kimiyya da fasaha na kasar Sin da ke shafar matsakaici da dogon wa'adi mai zuwa", yadda za a yi tsimin makamashin halittu a kan gine-gine da gina sabbin gine-gine marasa kazamtarwa suna daya daga cikin muhimman ayyukan da za a kara mai da hankali a kansu wajen raya birane. Bisa ka'idojin da aka tsara a cikin wannan tsari, a nan gaba, dole ne a bi sabon ma'aunin tsimin makamashin halittu kan sabbin gine-gine."

Domin ciyar da aikin gina gine-gine masu kazamtarwa kuma masu yin tsimin yin amfani da makamashin halittu gaba, gwamnatin kasar Sin ta tsara kuma ta bayar da ma'aunonin tsimin makamashin halittu. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta riga ta fara yin gwaji a yankuna 19 ciki har da larduna da jihohi masu cin gashin kansu da manyan biranen da ke karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya kai tsaye a kan gine-ginen da fadinsu ya kai kusan murabba'in mita miliyan 5. Sannan kuma, gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan aikin yin nazarin fasahohin tsimin makamashin halittu. Yanzu wasu aiki sun riga sun samu ci gaba sosai sakamakon taimakon da aka samu daga hannun gwamnatin, har an riga an fara yin amfani da fasahohin tsimin makamashin halittu a kan gine-gine, alal misali, an fara yin amfani da ruwan da ake sake amfani da shi da fasahar kiyaye yawan zafi a cikin bangon gine-gine da dai sauransu.

Bisa kididdigar da aka yi, a cikin gine-ginen da fadinsu ya kai murabba'in mita biliyan 40, dole ne a kyautata gine-ginen da suka kai fadin murabba'in mita fiye da biliyan 13 domin tsimin makamashin halittu. Sabo da haka, ana da damar kasuwanci kwarai. A gun taron baje koli na kayayyakin da suke tsimin makamashin halittu da aka yi a nan birnin Beijing a kwanan baya, Mr. Wu Shutian wanda ya zo daga kamfanin yin nazari da yin gilas na Beijing, inda ke yin nazari kan gilishi mai rike zafi wato Heat Mirror Insulating glass ya gaya wa wakilinmu cewa, "Halin musamman na wannan gilishi shi ne, idan an sa shi a tagogin gida, a lokacin zafi, ba za a ji zafi ba, a waje daya kuma, a lokacin sanyi, ba za a ji sanyi ba. Haka nan kuma, irin wannan gilas yana dacewa da yanayi daban-daban na duk duniya."

Mr. Wu ya ce, ya zuwa yanzu an riga an sa irin wannan gilishi a wurare da fadinsu ya kai murabba'in mita fiye da miliyan dari 1 a kan wasu sanannun gine-gine na kasashen duniya.

Makomar kasuwar raya kayayyakin tsimin makamashin halittu a kan gine-gine ta kasar Sin ta jawo hankulan kamfanonin kasashen waje sosai. Mr. Stephen Woodnutt, babban direktan kamfanin Delmatic da ya fi suna a duk fadin duniya a fannin yin kayayyakin tsimin makamashin halittu, ya gaya wa wakilinmu cewa, "Kasuwar raya gine-gine masu tsimin makamashin halittu ta kasar Sin tana jawo hankulanmu kwarai. Tsarin ba da haske da kamfaninmu ya yi yana dacewa da gine-gine iri iri. Sannan kuma, ba ma kawai za a iya sa tsarinmu a kan sabbin gine-gine ba, har ma za a sa shi a kan tsofaffin gine-gine."

Kan yadda za a raya fasahohin tsimin makamashin halittu a kan gine-gine, gwamnatin kasar Sin tana kokari sosai. An amince da cewa, a karkashin kokarin da gwamanti da masana'antu da 'yan kimiyya da fasaha suke yi tare, tabbas ne za a samu ci gaban ayyukan yin tsimin makamashin halittu a kan gine-gine. (Sanusi Chen)