Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-04 16:28:44    
(Sabunta)Kungiyar Hezbullah tana son daina harbar rakoki ga Isra'ila bisa sharadi

cri

A ranar 4 ga wata da alfijir, jiragen soja na Isra'ila sun jefa wasu boma bomai a kan yankunan da ke kudanci da arewacin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon. Wannan ya sa soja daya na gwamnatin kasar Lebanon ya mutu, mutane 3 sun ji rauni. Ban da wannan kuma, jiragen sama na sojojin Isra'ila sun jefa boma bomai a kan gadoji da yawa da ke arewacin birnin Beirut, wannan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 6.

Kafin haka, babban sakataren kungiyar Hezbullah Said Hasan Nasrallah ya yi wani jawabi a ran 3 ga wata inda ya ce, idan Isra'ila ta daina kai farmaki a kan kasar Lebanon, kungiyar Hezbullah a shirye take ta daina harbar rakoki a kan Isra'ila. To, wannan shi ne karo na farko da kungiyar Hezbullah ta nuna irin wannan bayani tun da suka fara rikici da juna.

A ran 3 ga wata, dakarun kungiyar Hezbullah sun harba rakoki fiye da 160 a kan Isra'ila, wannan ya sa mutane a kalla 7 sun mutu a yayin da mutane fiye da 30 suka ji rauni.

A ran nan, shugabannin mambobin kungiyar tarurruka ta musulunci sun shirya taron gaggawa, bayan taron sun bayar da wata sanarwa cewa, Isra'ila ta keta mulkin kai da cikakken yankin kasar Lebanon, kamata ya yi Isra'ila ta dauki dukkan nauyin da ke bisa wuyanta a sakamakon hari da ta kai wa Lebanon. Sanarwar ta sa kaimi ga kwamitin sulhu na MDD da ya gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya da zaman karko, da ya dauki matakai domin bangarorin Lebanon da Isra'ila su tsagaita bude wuta nan da nan.(Danladi)