Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-04 11:05:30    
Kungiyar Hezbullah tana son daina harbar rakoki ga Isra'ila bisa sharadi

cri

A ran 3 ga wata, ana ci gaba da rikicin da ke tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon. A ran nan, babban sakataren kungiyar Hezbullah ya yi wani jawabi inda ya ce, idan Isra'ila ta daina kai farmaki a kan kasar Lebanon, kungiyar Hezbullah a shirye take ta daina harbar rakoki ga Isra'ila. To, wannan shi ne karo na farko da kungiyar Hezbullah ta nuna irin wannan bayani tun da suka fara rikici da juna.

A ran nan da alfijir, jiragen soja na Isra'ila sun jefa wasu boma bomai a kan yankunan da musulmai 'yan rukunin Shi'a da ke kudancin birnin Beirut. Ban da wannan kuma, jiragen sama na Isra'ila sun jefa boma bomai a kan yankunan da ke kudancin kasar Lebanon da kudu maso gabashin kasar har sau fiye da 30. A ran nan kuma, sojojin Isra'ila kimanin dubu 10 sun shiga cikin kasar Lebanon, sun yi kazamin yaki da dakarun kungiyar Hezbullah a kauyuka 15.

A ran 3 ga wata, dakarun kungiyar Hezbullah sun harba rakoki fiye da 160 a kan Isra'ila, wannan ya sa mutane a kalla 7 sun mutu a yayin da mutane fiye da 30 suka ji rauni.

A ran nan, shugabannin mambobin kungiyar tarurruka ta musulunci kamar Malaysia da Indonisiya da Iran da Palesdinu da Lebanon da Sham sun shirya taron gaggawa a kasar Malaysia, bayan taron sun bayar da wata sanarwa cewa, Isra'ila ta keta mulkin kai da cikakken yankin kasa na Lebanon, kamata ya yi Isra'ila ta dauki dukkan nauyin da ke bisa wuyanta a sakamakon hari da ta kai wa Lebanon. Sanarwar ta sa kaimi ga kwamitin sulhu na MDD da ya gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya da zaman karko, da ya dauki matakai domin bangarorin Lebanon da Isra'ila su tsagaita wuta nan da nan.(Danladi)