Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-03 18:28:49    
Kungiyar OIC ta kira taro cikin gaggawa a kasar Malasiya domin yin tattaunwa kan matsalar gabas ta tsakiya

cri
A ran 3 ga wata, kungiyar taron musulmi wato OIC ta kira taron musamman a birnin Putrajaya, cibiyar harkokin siyasa ta kasar Malasiya domin yin tattaunawa kan hali mai tsanani da shiyyar gabas ta tsakiya ke ciki.

A gun bikin bude taron, Abdullah Ahmad Badawi, firayim ministan kasar Malasiya wadda ke rike da zagayan shugabannin kungiyar OIC ya yi kira ga kasashen musulunci da su aika da sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Lebanon, kuma ya kalubalanci dakarun kungiyar Hezbollah ta Lebanon da su tsagaita bude wutar yaki tsakaninsu da kasar Isra'ila nan da nan.

Bisa labarin da muka samu, an ce, an yi jigilar kayayyakin agaji na jin kai na rukuni na farko da gwamnatin kasar Sin ta samar ga gwamnatin kasar Lebanon a ran 3 ga wata daga birnin Beijing.

Bugu da kari kuma, sabo da bangarori daban daban da abin ya shafa ba su iya samun ra'ayi daya kan sa aya ga rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ba, shi ya sa an sake jinkirtar da lokacin kira taron duniya da aka tsai da yi a ran 3 ga wata domin kafa wata kungiyar sojojin kasashen gabas ta tsakiya. Haka kuma a ran 3 ga wata, Ehud Olmert, firayin ministan kasar Isra'ila ya bayyana cewa, bangaren Isra'ila yana ganin cewa, ya kamata a girke wata rundumar sojoji ta duniya da yawansu ya kai kusan dubu 15, ta yadda za a ba da taimako wajen kawo karshen yaki a tsakanin Isra'ila da dakarun kungiyar Hezbollah na Lebanon.(Kande Gao)