Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-03 18:23:04    
Jam'iyyar demokuradiyya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin

cri

An kafa Jam'iyyar demokuradiyya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin a watan Agusta na shekarar 1930. Manyan shugabannin kafa jam'iyyar su ne Deng Yanda da Huang Qixiang da Zhang Bojun. A watan Mayu na shekarar 1927, da yake kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kuomintang da ke birnin Wuhan na kasar Sin ya kudura niyyar cin amanar juyin juya hali, Zhen Yanda, shahararren shugaban masu sassaucin ra'ayi na jam'iyyar Kuomintang ya yi shirin kafa sabuwar jam'iyyar siyasa domin tafiyar da manyan manufofi 3 wato "yin hadin gwiwa da kasar Rasha da kuma J.K.S. da ba da taimako ga manoma da ma'aikata".

A shekarar 1935, Jam'iyyar demokuradiyya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin ta ja gaba wajen amsa "Sanarwar ran 1 ga Agusta" da J.K.S. ta bayar ta yin kira da a "daina yakin basasa, a yi dagiya da harin Japan", kuma ta kira taron ma'aikatan hukuma na 2 na duk kasa, bayan taron ta yi hadin gwiwa sosai a tsakaninta da J.K.S. A watan Fabrairu na shekarar 1947 kuma ta tsai da kudurin canja sunanta da ta zama Jam'iyyar demokuradiyya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin.

A watan Mayu na shekarar 1948, Jam'iyyar demokuradiyya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin ta mayar da martani ga kiran da kwamitin tsakiya na J.K.S. ta yi game da kafa sabuwar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, a watan Satumba na shekarar 1949 kuma ta aike da wakilanta don halartar taro na farko na dukkan wakilan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta farko ta jam''ar Sin, da zaben gwamnatin jama'a ta tsakiya. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, jama'iyyar ta tsai da tafarkin siyasa na yarda da shugabancin J.K.S. da yin hidima domin raya zaman gurguzu,

Bayan da aka shiga cikin sabon lokacin tarihi, Jam'iyyar demokuradiyya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin ta juya hankalinta kan muhimmin aikin raya zaman gurguzu na zamani, ta yin kokarin ba da shawarwari da ra'ayoyinta kan harkokin tattalin arziki da al'adu da likitanci. Yawancin mambobin Jam'iyyar su ne masanan ilmi wadanda suke da ikon wakilci a fannonin likitanci da kiwon lafiya. Yanzu yawan 'yan Jam'iyyar ya kai 70,657, shugaban Jam'iyyar kuma shi ne Jiang Zhenghua. (Umaru)