Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-03 17:35:57    
Bankin duniya ya tallafa wa masana'antun kasar Sin da su sarrafa kwal zuwa makamashi mai tsabta

cri

Hukumar hada-hadar kudi ta kasa da kasa wadda ke karkashin jagorancin bankin duniya za ta zuba jari ga kamfanin Xin'ao na kasar Sin, don mara masa baya wajen aikin sarrafa kwal zuwa wani irin makamashi mai kyau wanda ba zai gurbata muhalli ba. A jiya 2 ga wata, bangarorin biyu sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniya dangane da batun. Sabo da haka, wakilinmu da ke Washington ya ziyarci jami'an bangarorin biyu

Yayin da yake hira da wakilinmu, Lars Thunell, mataimakin darektan zartaswa na hukumar hada-hadar kudi ta kasa da kasa ya ce, hadin gwiwar da ke tsakanin hukumarsa da kuma kamfanin Xin'ao na kasar Sin zai bunkasa wani irin sabon makamashi, wanda zai biya bukatun kasar Sin a fannin makamashi kuma ba tare da gurbata muhalli ba. Al'amarin zai kasance wani muhimmin abu a kan hanyar neman makamashi mai tsabta a kasar Sin. Ya ce, 'kasar Sin tana da arzikin kwal, amma kona kwal da ake yi ba shi da kyau ga kiyaye muhalli. Idan mun canja kwal zuwa wani abin da ake kira dimethyl ether a bakin Turawa, wato DME a takaice, to, zai zama wani irin makamashi mai inganci kuma mai tsabta, musamman a wajen dafa abinci da dumama daki a gida, wanda zai amfana wa lafiyar jiki.'

A cewar masana, iskar DME makamashi ne mai tsabta, wanda ba zai fitar da hayaki mai guba ko sauran abubuwa ba a yayin da ake kona shi, kuma yana iya maye guraben kwal da katako a wajen samar da makamashi na dafa abinci da kuma dumama daki. Ban da wannan, idan a kwatanta shi da kwal, za a gane cewa, yawan iskar carbon dioxide da yake fitarwa a yayin da ake kona shi yana iya raguwa da kashi 40% bisa na kwal, wanda zai taimaka wajen daidaita matsalar dumamar yanayin duniyarmu. Sabo da haka, iskar nan ta DME ta zama wani sabon makamashi mai tsabta wanda ya jawo hankulan duniya a cikin 'yan shekarun nan.

Shugaban darektocin kamfanin Xin'ao na kasar Sin, Wang Yusuo ya ce, a halin yanzu dai, an fara yin amfani da iskar DME a wasu yankunan kasar Sin. Ya ce, 'wannan dai sauyi ne na hanyar zama. Kamar yadda kowa ya sani, gwamnatin kasar Sin tana kokarin bunkasa yankunan yammacin kasar, don neman wadatar da wuraren da ke fama da talauci tun da wuri.'

A ganin Mr.Wang, wannan na bukatar a daidaita batun bukatun mazauna wuraren yammacin kasar Sin a fannin makamashi, kuma bunkasa iskar nan ta DME wata dabara ce mai kyau. Bayan da aka sarrafa kwal wanda ake yawan samunsa a yammacin kasar Sin zuwa makamashi mai tsabta, to, abin zai amfana wa mazauna wurin da farkon fari. Ya kara da cewa, sakamakon tsarin makamashin kasar Sin na karancin mai da iskar gas, amma da arzikin kwal, bunkasa irin wannan makamashi mai tsabta na iskar DME da aka samo daga kwal zai taimaka wajen kyautata muhalli da kuma aikin samar da makamashi a kasar Sin. Ya ce, 'Tattalin arzikin kasar Sin yana bunkasa da sauri a cikin 'yan shekarun nan, kuma bakatu a fannin makamashi ma ya karu da sauri. A cikin irin wannan hali dai, tilas ne mu bunkasa makamashin da ke da halin musamman na kasar Sin, mu nemi samun kasancewar makamashi iri iri. Kuma a lokacin, mun tarar da karfin iskar DME a wajen maye gurbin man fetur da man gas, muna tsammanin tana da babbar kasuwa.' (Lubabatu Lei)