|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2006-08-03 15:17:35
|
|
(Sabunta) Sojojin sama na kasar Isra'ila sun kai farmaki kan karkarar kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon
cri
Ran 3 ga wata da sanyin safiya, jiragen sama na sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai farmaki kan sansanin dakarun kungiyar Hezbollah da ke yankin kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, amma har zuwa yanzu ba a samu rahoto game da mutanen da suka mutu ko jin rauni ba.
Ran 2 ga wata da sanyin safiya, sojojin Isra'ila sun maido da kai farmaki kan yankunan kasar Lebanon daga sama, bayan da suka dakatar da kai farmako kan kasar na awoyi 48. A wannan rana, Dan Halutz, babban hafsan hafsoshin sojojin tsaron kasar Isra'ila ya bayyana cewa, bangaren Isra'ila ba zai tabbatar da tsagaita bude wuta da kungiyar Hezbollah ba, yanzu sojojin Isra'ila suna yin la'akari da kara kai farmaki kan yankunan kasar Lebanon.
A sa'i daya kuma, ran 2 ga wata, 'yan dakarun kungiyr Hezbollah su ma sun kai farmaki da makaman roka kan kasar Isra'ila, wanda ya fi girma a rana daya tun bayan da aka tayar da rikicin tsakanin Lebanon da Isra'ila. Sakamkon haka, mutum daya ya mutu, yayin da 19 suka jin rauni.
Ran 2 ga wata, Ahmed Fawzi, kakakin babban sakataren M.D.D. ya sanar da cewa, an kara jinkirtar da lokacin kira taron duniya dangane da shirya wata kungiyar sojojin kasashen Gabas ta tsakiya da aka tsada kudurin aiwatarwa a ran 3 ga wata a babban hedkwatar M.D.D., sabo da bangarori daban daban da ke da nasaba ba su shirya wani shirin da ke iya kawo karshen rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila ba. Ran 3 ga wata, Ehud Olmert, firayin ministan kasar Isra'ila ya bayyana cewa, bangaren Isra'ila yana ganin cewa, ya kamata a girke wata rundumar soja ta duniya da yawan sojojinta ya kai kamar dubu 15, domin ba da taimako wajen kawo karshen yaki a tsakanin Isra'ila da dakarun kungiyar Hezbollah na Lebanon. (Bilkisu)
|
|
|