Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-03 12:01:24    
Sojojin sama na kasar Isra'ila sun kai farmaki kan karkarar kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon

cri
Ran 3 ga wata da wuri, jiragen sama na sojojin Isra'ila sun soma kai farmaki kan sansanin dakarun kungiyar Hezbollah da ke yankin kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar Lebanon, amma har zuwa yanzu ba a samu rahoto game da mutanen da suka mutu ko jin rauni ba.

Ran 2 ga wata da sanyin safiya, sojojin Isra'ila sun maido da kai farmaki kan takitin da ke shiyyar Lebanon daga sama, bayan da suka dakatar da kai farmako kan kasar na awoyi 48. A wannan rana, Dan Halutz, babban hafsan hafsoshin sojojin tsaron kasar Isra'ila ya bayyana cewa, bangaren Isra'ila ba zai tabbatar da tsagaita bude wuta da kungiyar Hezbollah ba, yanzu sojojin Isra'ila suna yin la'akari da kara kai farmaki kan yankunan kasar Lebanon.

A sa'i daya kuma, ran 2 ga wata, 'yan dakarun kungiyr Hezbollah su ma sun kai farmaki da makaman roka kan kasar Isra'ila, wanda ya fi girma a rana daya tun bayan da aka tayar da rikicin tsakanin Lebanon da Isra'ila. Sakamkon haka, mutum daya ya mutu, yayin da 19 suka jin rauni.

Ran 2 ga wata, Ahmed Fawzi, kakakin babban sakataren M.D.D. ya sanar da cewa, an kara jinkirtar da lokacin kira taron duniya dangane da shirya wata kungiyar sojojin kasashen Gabas ta tsakiya da aka tsada kudurin yinsa a ran 3 ga wata a babban hedkwatar M.D.D..

Bisa labari daban da muka samu an ce, ran 2 ga wata, Emile Lahud, shugaban kasar Lebanon ya zargi kasar Amurka da rashin yin kokari sosai, domin warware rikicin kasashen Lebanon da Isra'ila da ke kasancewa a yanzu ba. (Bilkisu)