An labarta, cewa wakilin din-gin-din na kasar Rasha dake Majalisar Dinkin Duniya Mr. Vitaly Churkin ya furta, cewa shelar dakatar da inganta sinadarin Urainium cikin gajeren lokaci da kasar Iran za ta yi tana da muhimmancin gaske ga samun sulhu tsakanin bangarori daban daban game da maganar nukiliyar Iran.
Mr. Churkin ya kuma ce, bisa jerin ra'ayoyin da jami'an Iran suka bayyana, ana ganin, cewa gwamnatin Iran tana la'akari da yin shawarwari tare da bangarorin da abun ya shafa, amma ba ta da shirin dakatar da inganta sinadarin Urainium cikin gajeren lokaci. Mr. Churkin ya jaddada, cewa bangarori daban daban za su kasa samun shirin shiga tsakani idan Iran ba ta dakatar da inganta sinadarin Urainium cikin gajeren lokaci ba. ( Sani Wang)
|