Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-02 17:34:48    
Tsatson Huang Di da Yan Di

cri

Yau da shekaru kimanin dubu biyar da suka shige, kakanin-kakanin Sinawa suka yi zama a wuraren dake dab da haddin ruwa na Rawayen Kogi, kuma sun rabu cikin wassu kabilu. An ji labarin, cewa daga cikinsu, akwai shugabanni na kabilu biyu. Daya sunansa Huang Di, daya kuma shi ne Yan Di. Su 'yan-uwa ne. Uwarsu daya, amma ubansu ba daya ba. A wancan lokaci, akwai kuma wata kabila, sunan shugabanta shi ne Chi You. Lallai fuskar ' yan kabilar nan tana da ban tsoro. Ga shi kawunansu na tagulla ne kuma jikinsu kaman na naman daji ne ; kuma abincinsu rairayi da duwatsu ne ; Ban da wannan kuma suna da bindigoyi da yawa kuma suna iya maita. Chi You ya kan jagoranci 'yan kabilarsa don kai hari ga sauran kabilu, wadanda suka kasa yin dagiya da su. Ban da wannan kuma, ' yan kabilar Chi You sun mamaye wuraren ' yan kabila na Yan Di, wanda kuma ya ga tilas ne ya tsere zuwa wurin Huang Di domin neman taimako.

Sai Huang Di ya umurci kabilu dabam daban da su kera bindigogi cikin gaggawa yayin da ya tura wani jarumi mai suna Ying Long don kama manyan dabbobi, wadanda kuma suka bi umurnin Ying Long an jima kadan bayan wannan lokaci. Sai Ying Long ya kirayi dabbobin da su yi kwanto sosai kan hanya bisa umurnin Huang Di, kuma shi kansa ya jagoranci ' yan kabilu dabam daban don yin yaki da Chi You. A karshe dai, sun kashe Chi You. Lallai Huang Di ya yako babbar nasara. Mutane duk sun fadi, cewa Huang Di dan sarkin samaniya ne, sun kuma ba da shawarar zaben Huang Di don ya zama shugaban kawancen kabilu.

Daga wannan lokaci ne mutane suke kiran Huang Di dan aljanna, wanda ya jagoranci jama'ar kabilu dabam daban ga yin sujadar girmamawa ga samaniya da kasa da kuma gunki, da yin aiki tsakani da Allah wajen bunkasa sha'anin noma da al'adu. Huang Di ya kafa dokar kalanda ta gargajiya da ba a taba ganin irinta ba a tarihin kasar Sin. Ana kiranta " Kalandar Huang". Ban da wannan kuma ya yi nazarin ilmin likitanci tare da mashahurin llikita mai suna Qi Bo. Daga baya, tsatsonsu sun rubuta wani littafi bisa hasashensu . Kazalika, Huang Di ya aika da matarsa da ta koyar da jama'a afannin kiwon tsuntsayen siliki don dinka kyawawan tufafi. A karkashin jagorancin Huang Di ne jama'a suka gina gidaje da kera motoci da kwale-kwale da kuma makamai na tagulla. Lallai wuraren dake dab da Rawayen Kogi sun zama zauren al'adu na tsohon zamanin da na kasar Sin, kuma ya zama daya daga cikin mafaran samun al'adu na can can da na 'yan adam.

Kabilun dake wuraren haddin ruwa na Rawayen Kogi suna kiran kansu " Al'ummar Hua" ko " Al'ummar Huaxia". Jama'ar kabilar Huaxia sun yada al'adu zuwa wurare dabam daban na duk kasa. Saboda haka, al'ummar kasar Sin ta zama babban sunan kabilu dabam daban na kasar Sin.

Al'ummar kasar Sin ta girmama Huang Di kwarai da gaske, kuma ta dauki Huang Di a matsayin kakani-kakanin al'ummar Huaxia. Da yake kabilar Yan Di da kabilar Huang Di sun hadu, shi ya sa Sinawa suke kiran kansu " Tsatson Huang Di da Yan Di". ( Sani Wang )