Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-02 17:32:35    
Wasu tambayoyi daga kungiyar masu sauraronmu ta Sokoto

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun mai sauraronmu na kullu yaumin daga kungiyar masu sauraronmu ta jihar Sokoto ta tarayyar Nijeriya, wato shugaba Bello Abubakar Malami Gero. A cikin wasikar da ya rubuto mana, ya yi mana wasu tambayoyi hudu. Wato shin yanzu Sinawa nawa ne ke jin Hausa a sashen Hausa na rediyon kasar Sin da kuma kasar Sin baki daya. Mene ne nukiliya da nake jin ana ta fadi har ma ana haramta kera shi, kuma kasa nawa ne ta mallake shi a duniya? Sa'an nan kuma, mene ne kwatan-kwacin kudin kasar Sin da na Nijeriya, Amurka, Ingila, Faransa da kuma Jamus. Tafiyar sa'o'i nawa ne daga Nijeriya zuwa kasar Sin, kuma nawa ne ake kashewa kafin a sami isa kasar Sin?

A hakika, game da farkon tambayoyi guda biyu da shugaba Bello ya yi mana, da ma wasu masu sauraronmu sun taba yi mana tambayoyi irin wannan, kuma mun taba ba ku bayani sosai a cikin wannan fili namu na amsoshin wasikunku. Shi ya sa a cikin shirinmu na yau, za mu ba ku takaitaccen bayani kawai a kansu.

Lokacin da Hausawa suka gamu da Sinawa wadanda ke iya Hausa, kullum su kan ji mamaki. Amma hasali ma dai, tun tuni a shekarun 1960, don neman nuna goyon baya ga aikin neman 'yancin kan al'umman kasashen Afirka, Sinawa sun fara koyon Harsunan kasashen Afirka, ciki har da harshen Hausa. A shekara ta 1964, a hukunce ne aka kafa sashen karanta Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing. Daga baya kuma, jami'ar ta yi ta daukar dalibai kusan a shekaru hudu hudu don su koyi Hausa. Ya zuwa yanzu dai, yawan Sinawa da suke jin Hausa ya kusanci 100. A sashen Hausa na rediyon kasar Sin ma, bi da bi ne ma'aikata Sinawa kimanin 20 sun taba aiki a wurin, a halin yanzu dai, akwai ma'aikata Sinawa 10 a sashen Hausa.

A kan batun nukiliya, da farko dai, muna so mu dan bayyana muku sinadarin Uranium. Uranium dai atom ne da ya fi nauyi a duniya. A shekaru 50 da suka wuce, masanan ilmin kimiyya sun gano wani irin Uranium mai nau'in U-235 wanda ke iya fashewa idan ya hadu da wani neutron, kuma a sa'in da yake fashewa, yana iya fitar da makamashi masu yawan gaske, wato aikin da muke kira nuclear fission ke nan. Idan Uranium ya fashe, zai iya fitar da makamashi mai yawan gaske, alal misali, idan mun kwatanta shi da kwal, yawan makamashin da U-235 gram 1 ke iya fitarwa ya tashi daya da makamashin da kwal masu inganci da nauyinsu ya kai ton 2 da rabi ke iya bayarwa idan an kone su kwata-kwata. To, irin makamashi mai yawan gaske shi ne makamashin nukiliya. Atom bom shi ne ke amfani da irin dimbin makamashin da ake samu daga fashewar atom a wajen kawo barna. Amma dai sabo da irin karfi mai ban tsoro da ke iya kawo barna, shi ya sa gamayyar kasa da kasa ke kokarin neman haramta kera makaman nukiliya. A halin yanzu dai, yawanci ana ganin cewa, kasashen da ke mallakar nukiliya su ne Amurka da Rasha da Faransa da Ingila da Sin da Indiya da Pakistan da kuma Isra'ila. Amma ban da makaman nukiliya, nukiliya shi ma ya kawo mana wani irin sabon makamashi mai kyau wanda ke da tsabta da kuma tattali., wato makamashin nukiliya.

To, yanzu bari mu amsa tambaya ta uku ta shugaba Bello. Wato mene kwatan-kwacin kudin Sin da na Nijeriya, Amurka, Ingila, Faransa da kuma Jamus. A halin yanzu dai, kudin Sin yuan daya ya tashi daya da Naira kimanin 16, a yayin da kwatan-kwacin kudin Sin da dallar Amurka da kuma kudin Euro ya kai 8:1 da kuma 10:1.

Game da lokacin tafiya daga Nijeriya zuwa kasar Sin, wannan ya danganta ga hanyoyi daban daban da jiragen sama na kamfanoni daban daban suke bi. Ga misali, idan ka shiga jirgi na kamfanin jiragen sama na Habasha, ka tashi daga birnin Lagos, sa'an nan ka bi ta biranen Adis Ababa da kuma New Delhi, ka isa birnin Beijing, babban birnin kasar Sin daga karshe, lokacin zai kai kimanin sa'o'i 19. Idan kuma ka shiga jirgi na kamfanin jiragen saman Birtaniya, ka tashi daga Lagos, sa'an nan ka yada zango a London, daga karshe kuma ka sami isa Beijing, to, za ka kashe sa'o'i 15 a kan hanya ke nan. A nan muna magana a kan lokacin tafiya, wanda bai hada da lokacin tsayawa ba. Kudin da aka kashe ma ya danganta ga hanyoyi daban daban da aka zaba, amma ba zai wuce dallar Amurka 1,600 ba a iyaka.