Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-02 16:50:11    
Jirgin sama na musamman da ya dauko akwatin gawar Du Zhaoyu ya iso birnin Beijing

cri

A ran 2 ga wata da karfe 10 da safe, jiragen sama na musamman da kwamitin aikin soja na tsakiya na kasar Sin ya tura wanda ya dauko akwatin gawar Du Zhaoyu, Basine mai lura da al'amura na MDD wanda ya rasa ransa a kasar Lebanon ya iso nan birnin Beijing. Kungiyar da ke kunshe da wakilai shida wadanda ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasa ta Sin da ma'aikatar harkokin waje ta kasar suka tura don daidaita wannan al'amari da Madam Li Lingling, matar marigayi Du Zhaoyu su ma sun komo gida cikin wannan jirgin sama na musamman.

Zhang Qinsheng, mai ba da taimako ga babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Sin da Cui Tiankai, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na Sin da iyayen Du Zhaoyu da kuma dansa sun je filin jiragen sama don karbar akwatin gawar Du Zhaoyu da ya koma gida. (Kande Gao)