Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-02 14:45:09    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(27/07-02/08)

cri
A cikin karon karshe na gasar cin kofin Asiya ta wasan kwallon kafa ta mata ta karo na 15 da aka yi a ran 30 ga watan Yuli da yamma, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta lashe kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Australia, shi ya sa ta zama zakara. Bangarorin 2 sun yi kunnen doki da ci 2 da 2 a cikin mintoci 120. A cikin gasar buga kwallo daga kai sai mai tsaron gida da suka yi, mai tsaron gida ta kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin Zhang Yanru ta kabar da kwallaye 2, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin kuma ta tura dukan kwallaye 4 cikin ragar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Australia. A sakamakon haka, kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta zama zakara da ci 6 da 4. Ban da wannan kuma, 'yar wasan kasar Sin Ma Xiaoxu ta zama 'yar wasa mafi nagarta a wannan gami.

An rufe gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur ta matasa da yara ta Asiya ta karo na 12 a Kitakyushu na kasar Japan a ran 30 ga watan Yuli. A cikin karon karshe na gasannin tsakanin mutum dai dai na rukunonin matasa da kuma yara da aka yi a ran nan, kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta sake samun lambobin zinare 3. Saboda haka, kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta sami lambobin zinare 7 da azurfa 3 a cikin dukan kananan wasanni 10.

Ran 30 ga watan Yuli, a cikin karon karshe na budadiyyar gasar wasan kwallon badminton ta kasar Thailand da aka yi a birnin Bangkok, hedkwatar kasar, 'yan wasan kasar Sin Chen Yu da Zhu Lin sun lashe 'yan takararsu daya bayan daya, Chen Yu ya zama zakara a cikin gasa ta tsakanin namiji da namiji, Zhu Lin ta zama zakara a cikin gasa ta tsakanin mace da mace, wani dan wasan kasar Sin daban Chen Jin ya zama na biyu a cikin gasar tsakanin namiji da namiji.

Ran 25 ga watan jiya, a nan Beijing, babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta gabatar da shirye-shirye kan yadda za a bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na kasar Sin a cikin shekaru 5 masu zuwa.

A cikin shirye-shiryen da kasar Sin ta tsara, an gabatar da cewa, za a yi amfani da damar shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing wajen daga matsayin da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa a kai a fannin kara samar wa jama'ar kasar Sin ayyukan hidimomi da suka shafi wasannin motsa jiki, kamar su samar musu wuraren motsa jiki da kayayyakin motsa jiki da dai sauransu. A sa'i daya kuma, za a yi amfani da zarafin shiryawa da kuma shiga cikin taron wasannin Olympic na Beijing wajen daga matsayin kasar Sin a fannin wasannin motsa jiki daga duk fannoni.(Tasallah)