Wakilin Rediyon kasar Sin ya aiko mana labari cewa , a ran 1 ga watan nan , Yaki tsakanin kasar Isra'ila da Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon yana ci gaba . Bangarorin biyu sun sami rauni da mutuwa. A wannan rana , ministocin harkokin waje na Kungiyar tarayyar Turai sun yi taron musamman , inda suka yi kira ga banrarorin biyu da su sasauta.
A ran 1 ga watan sojojin Isra'ila da dakaru masu dauke da makamai na Kungiyar Hezbollah sun yi musayar wutar yaki a wani Kauyen dake iyakar kudancin kasar Lebanon , ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 3 na kasar Isra'ila . Sauran sojoji 25 sun ji rauni .
A wannan rana Kungiyar tarayyar Turai ta yi taron musamman a birnin Brusel , kuma ta bayar da sanarwa , inda ta yi kira ga bangarorin biyu da su yi shirin tsagaita bude wuta cikin dogon lokaci . Erkki Tuomioja , ministan harkokin waje na kasar Finland , kasar shugaban Kungiyar tarayyar Turai ya jaddada cewa , ya kamata Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin gaggawa don hana yaduwar yakin tsakanin bangarorin biyu . A shirye suke kasashen Turai su shiga aikin kiyaye zaman lafiya . (Ado)
|