Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-01 20:12:00    
Marmaron ruwa mai zafi na Yongning

cri

A wannan mao ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu n ayau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan marmaron ruwan zafi na Yongning, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, kai ziyara ga dakin nune-nunen dukiyoyi a fadar sarakuna na Beijing wato Forbidden City.

Marmaron ruwa mai zafi na Yongning yana cikin kwari na Yongning na birnin Lijiang na lardin Yunan na kasar Sin, wanda manyan duwatsu suna kewayensa, 'yan kabilun Mousou da Pumi sun gina gidajensu a gindin wadannan manyan duwatsu. Ruwa mai zafi ya fito daga gindin babban dutse mai suna Wadu, yana da tsabta sosai, ana yi wanka a duk shekara.

Fadin marmaron ruwa mai zafi na Yongning ya kai misalin muraba'in mita 50, zafin ruwa da ya fito daga wannan marmaro ya kai digiri 37 a ko wane lokaci. Marmaron ruwa mai zafi na Yongning ya yi suna ne har tsawon shekaru daruruka, wanda wurin wanka ne na halittu mai kyau. Ruwa mai zafi da ya fito daga wannan marmaro yana da amfani sosai a fannin shawo kan amosanin gabbai da ciwon fata. An ce, a da wannan marmaro yana kudu maso yammacin garin Yongyu, daga baya, ya kaura zuwa Yongning saboda motsin tsalar duniya. Bisa almarar da aka bayar, da can ruwan da ke fito daga wannan marmaro yana da zafi sosai, ba a iya yin amfani da shi ba, amma ya yi sanyi sannu a hankali, yanzu zafin ruwan ya fi dace da wanka ga mutane.

Kafin shekaru 60 na karni na 20 da suka gabata, saboda zirga-zirga da kuma mu'amalar al'adu suna baya, mutanen wurin ba safai su kan yi mu'amala da mutanen sauran wurare ba, sun saki jiki, sun taimakawa juna zuwa wannan marmaron ruwa mai zafi tare, inda suka yi wanka tare, su sha giya tare, su yi musayar abinci, su yi wa juna gaisuwa, su yi hira kan zaman rayuwarsu na yau da kullun, su rera wakokoki tare, sun ji dadi sosai.

Marmaron ruwa mai zafi na Yongning cike yake da al'adun kabilu. Kauyukan Walabi da Yimanwa da Aruwa da Aguwa da 'yan kabilar Muosou ke zama sun kewaye wannan marmaro. Idan ana kai masa ziyara, ba ma kawai za a iya yin shakatawa a cikin ruwa mai zafi ba, har ma za a ji al'adun kabilu a rai.