Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-01 18:44:54    
Kai ziyara ga dakin nune-nunen dukiyoyi a fadar sarakuna na Beijing wato Forbidden City

cri

Ming da Qing suka zauna. Wannan fada babban baitulmali ne a fannin al'adun kasashen gabas saboda manyan gine-ginen gargajiya da tsoffin kayayyakin tarihi masu daraja fiye da miliyan daya da aka ajiye a nan. A cikin shirinmu na yau na yawon shakatawa a kasar Sin, za mu kai ziyara ga wani dakin musamman wato dakin nune-nunen dukiyoyi, inda aka nuna tsoffin kayayyakin tarihi mafiya daraja, Dakin nune-nunen dukiyoyi yana cikin fada mai suna Ningshouquan da ke gabashin fadar sarakuna. An raba dakin nune-nunen dukiyoyi zuwa sassa 6, fadinsu ya kai muraba'in mita dubu 2 da dari 2. Tsoffin kayayyakin tarihi 311 da aka nuna a nan wadanda aka zabe su ne daga tsoffin kayayyakin tarihi masu yawa da ke cikin wannan fadar sarakuna. Darektan sashen kayayyakin gargajiya na fadar sarakuna na kasar Sin madam Zhang Rong ta ba da karin haske cewa, yawancin dukiyoyin da aka nuna a nan kayayyaki kurum da ke kasancewa a duniya, kuma suna da daraja sosai, har ma ba a iya kwatanta su da kudi ba. Wadannan kayayyakin fasaha da aka kera da zinare da azurfa da da duwatsun lu'ulu'u iri daban daban da sauran duwatsu masu daraja sun nuna matsayin koli da masu fasaha suke tsayawa a kai a lokacin nan.

Wadannan dukiyoyi sun hada da kayayyakin yau da kullum masu yawa da a kan yi a fadar sarakuna, a cikinsu kuma akwai wani kofi na farin dutsen lu'ulu'u na jade, wanda marfi da faranti tasa aka yi da zinare. An yi wannan kofi da wani farin dutsen lu'ulu'u, an kuma ajiye shi a kan farantin zinare, sai ka ce wani farin furen lotus. Akwai irin wadannan kayayyakin dutsen lu'ulu'u na jade da yawa a cikin dakin nune-nunen dukiyoyi. Madam Zhang Rong ta yi bayanin cewa, dukan wadannan kayayyakin dutsen lu'ulu'u na jade masu kyau gani sun zo daga Hetian na jihar Xinjiang mai ikon tafiyar da harkokinta da kanta ta kasar Sin, wanda ya yi suna ne sabada dutsen lu'ulu'un jade. Ta ce,''dutsen lu'ulu'u na jade na Hetian na daya daga cikin duwatsun lu'ulu'u na jade mafiya kyau, wanda aka samu daga ruwa. Kansa yana haske, kamar mai yana haske. Wadannan kayayyakin dutsen lu'ulu'u na jade na Hetian suna da daraja sosai da sosai.'

Kayayyakin da iyalan sarakuna suka yi amfani da su da aka nuna su a cikin dakin nune-nunen dukiyoyi ba ma kawai an kera su da duwatsun lu'ulu'u, har ma zane-zanensu suna da fasaha, an kera su yadda ya kamata.

Yawancin tsoffin kayayyakin tarihi da ke cikin dakin nune-nunen dukiyoyi ba a san asali da tarihinsu sosai ba, saboda suna da dogon tarihi, amma wasu daga cikinsu sun yi rajista, kamar su tambura 3 na dutsen Tianhuang da aka hada su tare. Tianhuang wani iri dutes ne da aka samu a lardin Fujian na kasar Sin, launinsa rawaya mai cizawa, a cikinsa kuma akwai wani farin abu, da can Sinawa su kan ce, darajar dutsen Tianhuang gram 0.05 ta yi daidai da ta zinare gram 0.15, ya zuwa yanzu farashin dutsen Tianhuang yana da tsada kwarai, farashinsa na gram 1 ya kai misalin kudin Sin yuan dubu. Dalilin da ya sa wadannan tambura 3 na dutsen Tianhuang suna da matukar daraja shi ne saboda an hada wadannan tambura 3 da sarkoki, kuma an sassaka wadannan tambura 3 da sarkoki daga wani dutsen Tianhuang daya. Mutane sun yi mamaki kwarai domin girman wannan dutse da kuma wuyar aikin sassaka.

Dakin Shoule, wani muhimmin gini ne da ke cikin dakin nune-nunen dukiyoyi, inda sarauniya Ci Xi ta karshen zamanin daular Qing ta taba zama a nan a lokacin da take tsohuwa, ma iya mayar da wannan daki daki ce da ta fi jin dadin jama'a a cikin fadar sarakuna, saboda an yi masa ado da zane-zane da enamel. Yanzu an nuna wasu manyan kayayyaki a nan, wadannan suka hada da wani sassakar dutsen lu'ulu'u na jade mafi girma a duk fadar sarakuna, wato dutsen lu'ulu'u na jade da aka sassaka bisa labarin Da Yu, wanda ya daidaita matsalar ambaliyar ruwa. Tsayin wannan babban dutsen lu'ulu'u ya kai mita 2, nauyin sa ya kai ton 5, an ajiye shi a nan har tsawon shekaru fiye da 200. An ba da karin haske cewa, an jigilar da danyen dutsen lu'ulu'u na jade daga babban dutsen Mi Le Ta na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin zuwa Beijing, daga baya, zuwa birnin Yangzhou da ke kudancin kasar, inda masu fasahar sassakar dutsen lu'ulu'u na jade ta zamani suka sassaka shi, bayan haka, an komar da shi a nan Beijing, an yi shekaru 10 ana yin wannan aiki, kuma ba a iya kidaya mutane da kudaden da aka yi amfani da su domin wannan babban aiki ba.

Dukan masu yawon shakatawa su kan yi mamaki sosai saboda wannan babbar dukiya, Mr. Travis, dan kasar Amurka ya bayyana cewa, ya fi son wannan babban kayan dutsen lu'ulu'u a cikin dukan dukiyoyin da ke nuna a cikin dakin nune-nunen dukiyoyi, ya ce, 'wannan tsohon sassaka yana da mamaki, ina jin sha'awa kwarai, an sassaka da kuma shirya shi yadda ya kamata.'