Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-01 18:41:04    
Kasar Sin tana kokarin tabbatar da yin amfanin da albarkatun ruwan Rawayan kogi cikin hali mai dorewa

cri

Tun daga yau, ran 1 ga watan Agusta, an fara tafiyar da "Ka'idojin raba ruwan Rawayan kogi" da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar kwanan baya. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta kafa doka kan yadda za a raba da yin amfani da ruwan manyan koguna.

Rawayan kogi da yake ratsa larduna da jihohi 9 da suke arewa maso yammaci da arewancin kasar Sin kogi ne mafi tsawo na biyu a kasar Sin. Fadin wuraren da yake ratsawa ya kai murabba'in kilomita fiye da dubu dari 7, wato yana shafar gonakin da suka kai kashi 15 daga cikin dukkan gonakin kasar da mutanen da suka kai kashi 12 daga cikin dukkan yawan mutanen kasar. Yanzu, wadannan gonaki da mutane suna dogara da ruwan Rawayan kogin, inda ke cike da yashi, kuma yawan ruwansa yake samun sauye-sauye sosai a kowace shekara. Amma cikin shekaru 27 da suka wuce, wato tun daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1999, a yankunan karshen Rawayan kogi, a kan shiga cikin halin rashin ruwa a cikin kogin. Ya zuwa yanzu, yawan ruwan Rawayan kogi da aka dauka ya riga ya kai fiye da kashi 60 cikin kashi dari. Mai yiyuwa ne za a shiga halin rashin ruwa a cikin kogin a kowane lokaci. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta bayar da wadannan "Ka'idojin raba albarkatun ruwan Rawayan kogi" domin kara sarrafa halittun ruwan Rawayan kogi ta hanyar shari'a.

A gun wani taron manema labaru da aka yi a ran 1 ga wata, Kao Fengtao, mataimakin shugaban ofishin tsara dokoki na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ce, lokacin da aka tsara "Ka'idojin raba albarkatun ruwan Rawayan kogi", an bi ka'idojin hada moriyar tattalin arziki da ta zaman al'umma kuma da ta muhalli gaba daya. Mr. Kao ya ce, "Bisa 'Ka'idojin raba albarkatun ruwan Rawayan kogi' da aka tsara, lokacin da ake tsara shirin raba ruwan kogin, ya kamata a yi nazari kan yawan yashi da kogin zai kai su tare da ruwa a cikin teku da bukatun da zaman rayuwar jama'a da masana'antu da aikin gona da muhalli suke nema. Sannan kuma, ya kamata a yi amfani da hadadden amfani na albarkatun ruwan Rawayan kogi domin tabbatar da cewa za a iya yin amfani da albarkatun ruwan Rawayan kogi cikin hali mai dorewa. Sabo da haka, dole ne a yi nazari kan halin ruwan Rawayan kogi da ake ciki da tsarin raya yankunan da ke shafar kogin da tsarin samar da ruwa na matsakaici da na dogon lokaci kuma da halin da ake ciki game da yadda larduna da birane suke karbar ruwa daga kogin. "

Tun daga shekarun 90 na karnin da ya gabata, lokacin da yankunan da ke shafar Rawayan kogi suke samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, ya kasance da wasu matsaloli a tsakaninsu wajen yin amfani da albarkatun ruwan Rawayan kogi, har ma an haddasa cecekuce a tsakaninsu. Sabo da haka, bisa wannan "Ka'idojin raba albarkatun ruwan Rawayan kogi" da aka tsara, kwamitin kula da harkokin Rawayan kogi da gwamnatocin lardunan da ke shafar kogin ne su tsara shirin raba ruwan Rawayan kogi tare, sannan kuma, dole ne wannan shiri ya nemi amincewa daga majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

Bugu da kari kuma, an rubuta "Babi na neman daidaito cikin gaggawa" a cikin "Ka'idojin raba albarkatun ruwan Rawayan kogi" domin daidaita matsalar rashin samar da ruwa a kogin da za ta auku, inda aka nuna cewa, kwamitin kula da harkokin Rawayan kogi ne yake kulawa da aikin daidaita ruwa cikin gaggawa. Mr. Li Guoying, shugaban kwamitin kula da harkokin Rawayan kogi ya bayyana cewa, "Idan bala'in fari mai tsanani ya faru a cikin Rawayan kogi, kwamitin zai hada da sauran hukumomin da abin ya shafa domin bayar da shirin gaggawa wajen raba ruwan kogin. Bayan da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ko hukumar da abin ya shafa ta amince da shi, dole ne dukkan gwamnatocin larduna da sauran hukumomin da nasaaba da kogin su bi shirin gaggawa ba tare da neman kowane sharadi ba."

Li Guoying ya kara da cewa, lokacin da ake raba ruwa cikin gaggawa, an yarda da gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan rage yawan ruwan da ake dauka ko rufe bakin daukar ruwa da dai makamatansu. Ya kamata a yi kokari kan yadda za a hana sake bullowar matsalar rashin ruwa a cikin Rawayan kogi. Amma, a waje daya kuma, Mr. Li ya nuna cewa, wannan buri ne da ke da wuyar cimmawa. (Sanusi Chen)