Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-01 15:58:56    
(Sabunta) Majalisar ministoci ta kasar Isra'ila ta tsaida kudurin habaka aikin soja a shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon

cri

Ran 1 ga wata, majalisar ministoci ta kasar Isra'ila ta tsaida kuduri ta hanyar jefa kuri'o cewa, za ta ci gaba da fadada aikin soja na kasa a shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon.

Bisa shirin da majalisar ministoci ta kasar Isra'ila ta amince da shi, sojojin Isra'ila za su kara karfin kai farmaki kan shiyyar da ke kudancin kasar Lebanon, da murkushe sansanin 'yan dakarun kungiyar Hezbollah na Lebanon. A wannan rana kuma, jiragen sama na soja na kasar Isra'ila sun kai farmaki kan shiyyar da ke karkashin ikon 'yan dakarun kungiyar Hezbollah da ke kudancin kasar Lebanon, kuma sun kai farmaki kan hanyar zuwa kasar Sirya daga shiyyar da ke arewa maso gabashin kasar Lebanon.



Ran 31 ga watan Yuli, Ehud Olmert, firayin ministan kasar Isra'ila ya ce, ko da ya ke sojojin sama na Isra'ila sun tsaida kudurin dakatar da kai farmaki kan shiyyar da ke kudancin Lebanon daga sama a cikin awoyi 48, amma kasar Isra'ila ba za ta kawo karshen aikin soja da take yi wa kungiyar Hezbollah ba a cikin 'yan kwanaki masu zuwa. A wannan rana kuma, Fawzi Salloukh, ministan harkokin waje na kasar Lebanon ya sake nanata cewa, gwamnatin kasar Lebanon ba za ta yi ko wane irin shawarwari dangane da warware hargitsin Gabas ta tsakiya ba, idan ba a tabbatar da tsagaita bude wuta a tsakanin bangarorin Lebanon da Isra'ila ba. (Bilkisu)