A ran 31 ga watan jiya, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 1696 a sakamakon kuri'un amincewa 14 da kuri'ar kiyewa 1, inda aka bukaci kasar Iran da ta dakatar da dukkan ayyukan tace sinadarin Uranium kafin ranar 31 ga wata, haka kuma aka yi kira ga kasar Iran da ta gama kai da hukumar makamashin nukiliya ta duniya.
Wannan kuduri ya jaddada muhimmanci na warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar siyasa da diplomasiyya, kuma ya jaddada amfani mai muhimmanci na hukumar makamashin nukiliya ta duniya, kuma ya tabbatar da shirin da Amurka da Rasha da Sin da Ingila da Faransa da Jamus suka gabatar da shi.
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Liu Zhenmin ya ce, makasudin da kwamitin sulhu ya zartas da wannan kuduri shi ne domin kiyaye tsarin hana yaduwar makaman nukiliya da karfafa kwarjini da amfanin hukumar makamashin nukiliya ta duniya da kuma kara sa kaimi da a warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar siyasa da diplomasiyya.(Danladi)
|