Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-31 20:51:14    
Kundin sani na yara na farko da kasar Sin ta buga

cri

Watakila ku kan gamu da wasu yara masu son neman sani wadanda su kan yi tambayoyi bila adadin, har ma a karshe dai ba ku san yadda ya kamata ku ba su amsa ba. Iyayen yara na kasar Sin su kan gamu da irin wannan matsala. Amma yanzu wani littafi da ake kiran "Kundin sani na yara na kasar Sin" ya ba su taimako wajen warware matsalar. Bayan da aka buga littafin, nan da nan ne ya samu karbuwa sosai daga yara masu yawa, kuma a hankali a hankali ya riga ya zama wani malami kuma aboki na yara.

Masu sauraro, abin da kuka saurara dazun magana ce da dalibai biyu suka yi a gun wani taron aji na wata makarantar firamare ta birnin Beijing, wanda aka mayar da "tashi zuwa sararin sama bisa karfin kimiyya" a matsayin babban take. A gun wannan taron aji, dalibai sun yi wasan kwaikwayo da rawa, da nuna al'adun shayi na kasar Sin, da kuma amsa ilmin wasannin Olympic da dai sauransu.

Wata daliba ta ajin Xu Tong ta gaya wa wakilinmu cewa, dukkan shirye-shiryen nan su tsara su ne da kansu bisa ilmin da suka samu daga kundin sani na yara na kasar Sin. "kafin mu tsara wadannan shirye-shirye, da farko mu nemi abubuwa masu yawa da ke da nasaba da su a cikin kundin sani. Alal misali, fatar dan Adam ba ta iya kyautata a bayyane bayan da suka yi amfani da kayan kwaskwarimar fuska sau daya kawai, mun san ilmin ne daga kundin sani."

Kundin sani da ke cikin maganar Xu Tong shi ne Kundin Sani na Yara na Kasar Sin, wato wani kundin sani na farko da kasar Sin ta buga domin yara. Yau da shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta buga wannan kudin sani. Xu Tong ya gaya wa wakilinmu cewa, dalibai suna son kundin sani na yara na kasar Sin kwarai da gaske, yanzu a cikin ko wane aji na makarantar da take ciki, an ajiye irin wannan kudin sani domin a duba.

Kundin sani na yara na kasar Sin ya hade da littattafai uku, wato littafin halitta da na kimiyya da fasaha da kuma na zamantakewar al'umma. Kundin sani ya shafi fannoni daban daban, kamar sararin samaniya da halittu da hanyoyin zirga-zirga da al'adu da wasannin motsa jiki da tarihin dan Adam da dai sauransu. Amma abin da ya fi jawo hankalin yara shi ne a cikin littattafan nan, hotuna masu kyan gani da jimloli masu ban sha'awa sun sa yara su karbi wadannan ilmomi da sauki.

Ban da wannan kuma akwai ilmin zaman rayuwa na yau da kullum da kuma ilmin tsaron kai a cikin kundin sani. Iyayen yara sun darajanta wadannan ilmomi sosai.

Bisa Kidayar da aka yi, an ce, bayan da aka buga kundin sani na yara na kasar Sin, an riga an sayar da su da miliyan uku. Kuma abin farin ciki shi ne, yara masu yawa sun riga sun amfana daga littattaifan nan. Wata 'yar makarantar firamare ta birnin Beijing Liu Yichang ta gaya wa wakilinmu cewa "kudin sani ya ba ni taimako sosai. A wani karo, abokan iyayena sun je dakin ajiye kayan tarihi na kasar Sin tare da ni, daga baya kuma mun ga wasu fadi-ka-mutu, amma ba su san su mene ne ba, sai na gaya musu abubuwa game da fadi-ka-mutu da na samu daga kundin sani, dukkansu sun nuna mini yabo, sabo da haka ina yin murna kwarai da gaske. Yanzu na fi son kundin sani na yara na kasar Sin."

Saboda yara suna son kundin sani sosai, shi ya sa makarantun wurare daban daban na kasar Sin sun shirya harkokin da ke da nasaba da kundin sani. Alal misali, an watsa ilmin da ke cikin kundin sani ta rediyo da kuma shirya taron cudanya bayan da aka karanta kundin sani da dai sauransu.

Iyayen yara masu yawa sun bayyana cewa, ko da yake akwai littattafan yara da yawa a cikin kasuwar littattafai ta kasar Sin, amma littattafai masu koyar da ilmin kimiyya wadandan yara suka karbi sosai ba yawa. Kundin sani na yara na kasar Sin ya yi wani gwaji ne mai kyau wajen jagorancin yara kan neman sani. Suna fatan littattafai masu koyar da ilmin kimiyya masu yawa za su taka muhimmiyar rawa ga zaman yara a nan gaba. (Kande Gao)