Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-31 20:47:24    
Kabilar Achang ta kasar Sin

cri

Ana fi samun 'yan kabilar Achang a shiyyar Dehong ta kabilun Dai da Jingpo ta jihar Yunnan da ke kasar Sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin ta karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Achang ya kai fiye da dubu 30. 'Yan kabilar suna yin amfani da harshensu, wato harshen Achang, amma ba su da harafi, suna yin amfani da harafin kabilar Han da na kabilar Dai.

Bayan kafuwar kasar Sin, an kafa shiyyar kabilar Achang mai cin gashin kai a cikin shekara ta 1952 a yankin da aka fi samun 'yan kabilar da yawa. Tun lokacin kaka na shekara ta 1955, an yi gyare-gyaren gonaki ta hanyar yin shawarari cikin lumana a yankin kabilar Achang domin murkushe tsarin mallakan filaye irin na 'yan jari hujja kwata-kwata. Aikin gyare-gyaren gonaki ya fitar da talakawa na kabilar Achang daga hannun 'yan jari hujja, ta yadda aka ingiza bunkasuwar aikin samar da albarkatun gona.

Ban da wannan kuma gwamnatin kasar Sin ta bayar da taimako ga 'yan kabilar Achang kan kafa tashar yin allurar rigakafi da kuma horar da wasu likitoci na kabilar don tabbatar da lafiyar jikin 'yan kabilar.

Haka kuma an bunkasa sha'anin ilmi na kabilar Achang sosai. Ana iya samun malaman da suka gama karatunsu daga jami'o'in kasar Sin, kuma yara suna da damar shiga makaranta. Bayan taro na uku na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yi a cikin shekara ta 1978, an samun ci gaba kan sha'anin noma da masana'antun yin kayayyakin saka-saka da makamantansu sosai. Alal misali, an shuka shinkafa mai kyau a shiyyar Lianghe, kuma an gyara gonaki a shiyyar Hu Lache, ban da wannan kuma, an yi cinikayya iri daban daban wadanda dukkan mutanen gida da waje suke son sayen su sosai.

'Yan kabilar Achang su kan ci shinkafa da rogo da 'ya'yan lambu da nama a zaman yau da kullum, haka kuma dukkansu suna son cin abinci mai tsami sosai. A lokacin da, samari maza da mata su kan ci wani iri 'ya'yan itatuwa da ake kiransa betelnut a turanci, shi ya sa hakoransu su kan yi launin baki.