A ran 30 ga wata, a cikin halin kwanciyar hankali ne aka gama babban zaben shugaba da na majalisar dokoki na kasar Congo Kinshasha. Wannan ne karo na farko da aka yi babban zabe irin na dimokuradiyya a kasar tun bayan da ta samu 'yancin kai yau da shekaru 46 da suka wuce. Ko da yake, lokacin da aka yi babban zabe, akwai wasu kananan rikice-rikice, amma ba a haddasa tarzoma da matsalolin nuna karfin tuwo ba.
Bisa labarin da kwamitin kula da harkokin zabe mai 'yancin kai ta kasar Congo Kinshasha da kungiyar musamman ta M.D.D. wadda ke tabbatar da zaman lafiya a kasar suka bayar, an ce, a zauren tasoshin kuri'a dubbai da suke larduna da babban birni daya a duk fadin kasar, masu jefa kuri'a sun tafiyar da ikonsu ne cikin halin kwanciyar hankali. Ma'aikatun da ke kula da babban zabe da 'yan kallo da masu sa ido kan kuri'ar da aka zaba sun yi aikinsu ne yadda ya kamata.
Masu jefa kuri'a na kasar Congo Kinshasha sun jefa kuri'a ne cikin hali mai yakini. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da kungiyar musamman ta M.D.D. wadda ke tabbatar da zaman lafiya a kasar ta yi, yawan masu jefa kuri'a da suka jefa kuri'a a tasoshin kuri'a da ke birnin Kinshasha ya kai fiye da sittin cikin kashi dari. Bayan da suka jefa kuri'a, masu jefa kuri'a da yawa sun bayyana cewa, ya kamata su jefa kuri'arsu don makomar kasarsu.
A ran 17 ga watan Mayu na shekarar 1997, a karkashin goyon bayan kasashen Uganda da Rwanda, Laurent Kabila ya kori Mobuto wanda ya rike da ragamar mulkin kasar har na tsawon shekaru 32 daga mukaminsa. Lauren Kabila ya zama shugaban kasar. Amma a shekara ta biyu bayan da Lauren Kabila ya hau kan mukamin shugaban kasar, an haddasa yaki mai tsanani a kasar Congo Kinshasha, inda wasu kasashen makwabta suka sa hannu a ciki. A watan Afrilu na shekara ta 2003, bangarori daban-daban na kasar Congo Kinshasha sun sami ra'ayi daya kan yadda za a raba ikon mulkin kasar a cikin lokacin wucin gadi, sun kuma rattaba hannu a kan "Yarjejeniyar sulhuntawa daga duk fannoni" da "Tsarin mulkin kasar na lokacin wucin gadi". A watan Yuni da watan Agusta na shekara ta 2003, bi da bi ne aka kafa gwamnatin wucin gadi da kwarya-kwaryar majalisar dokokin kasa a Congo Kinshasha, inda Josef Kabila ya zaman shugaban wucin gadi na kasar. A watan Disamba na shekara ta 2005, an jefa kuri'ar raba gardama, inda aka zartas da sabon tsarin mulkin kasar Congo Kinshasha. A watan Afrilu na shekarar da muke ciki, gwamnatin wucin gadi ta Congo Kinshasha ta shelanta cewa, za a yi babban zabe ne a ran 30 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki.
A sa'i daya kuma, M.D.D. da kungiyar tarayyar Turai dukkansu sun tura sojojin tabbatar da zaman lafiya zuwa kasar Congo Kinshasha domin tabbatar da ganin an yi babban zabe lami lafiya. Bugu da kari kuma, kungiyar kawancen kasashen Afirka da kungiyar neman bunkasuwar kasashen kudancin nahiyar Afirka da kungiyar neman bunkasuwar tattalin arzikin kasashen da ke yankin tsakiyar Afirka da kungiyar kasashen Turai da wasu kungiyoyin shiyya-shiyya da kasashen Amurka da Afirka ta kudu da Japan sun tura 'yan kallonsu zuwa kasar Congo Kinshasha domin sa ido kan yadda ake shirya da yin babban zabe.
Mr. Charley, wani dalibi ne da ke karatu a wata jami'ar kasar. Bayan da ya jefa kuri'a, ya gaya wa wani manemi labaru cewa, "Kasarmu tana cikin hali maras kwanciyar hankali har na tsawon shekaru da yawa. Ba mu da sa'a sosai, kuma ba mu son a sake yin yaki. Yau, ya kamata mu jefa kuri'ar da ke cikin hannunmu, amma ba bindiga ko bindigar igwa ba domin zaben shugaban kasarmu."
Bayan da malama Chisha mai shekaru 49 da haihuwa ta jefa kuri'a a wata tashar kuri'a da ke kusa da fadar kasar Congo Kinshasha, ta gaya wa manemi labaru cewa, "Iyaye ba su da aikin yi, yara ma ba su iya shiga makaranta ba. Dole ne a sauya kasarmu da zaman rayuwarmu. Muna bukatar wani tabbataccen shugaba mai kokari."
Ko da yake, har yanzu, babban zaben da ake yi a kasar Congo Kinshasha zai fuskanci kalubale iri iri, alal misali, ko dukkan bangarori za su amince da sakamakon wannan babban zabe? Idan babu wani dan takara da ya ci zabe a zauren zagaye na farko na babban zabe, mene ne zai faru a zauren zagaye na biyu? Amma yanzu abin da aka amince da shi shi ne, kawo karshen yakin basasa kwata kwata har abada kuma da tabbatar da zaman lafiya a kasar Congo Kinshasha, buri ne da kowa yake son cimmawa. (Sanusi Chen)
|