Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-31 15:21:06    
Kasashen Isra'ila da Amurka suna fuskantar matsin da lamarin da ke faruwa a kauyan Gana ke kawo musu

cri

Ran 30 ga wata, jiragen sama na soja na kasar Isra'ila sun jefa boma-bomai daga sararin samaniya kan kauyen Gana da ke kudancin kasar Lebanon, sakamakon haka fararen hula 54 sun mutu, inda suka kunshi yara 37. Bayan faruwar lamarin, kasashen duniya sun yi mamaki sosai, kuma sun la'anci da nuna kiyewa kan kasar Isra'ila. A sa'i daya kuma, jama'a suna mai da hankali kan yaya kasashen Isra'ila da Amurka ke magance da matsin da lamarin kauyen Gana ke kawo musu.

A shekaru 10 da suka wuce, a kauyen Gana na kasar Lebanon, yaki ya taba barkewa kamar wannan lamari. A wancan lokaci, sojojin sama na kasar Isra'ila sun jefa boma-bomai kan wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kauyen Gana, sanadiyar haka, fararen hula 102 suka rasa rayukansu. Sabo da kasar Isra'ila da kasashen duniya sun matsawa Shimon Peres, firayin ministan kasar a lokacin, ya tsaida kudurin kawo karshen aikin soja. Amma, yanzu bayan faruwar lamari kamar wannan, kasar Isra'ila ta mayar da martanin bambanci.Ran 30 ga wata, Ehud Olmert, firayin ministan kasar Isra'ila ya nuna bakin ciki kan mutuwar fararen hula bisa sanadiyar jefa boma-bomai, a sa'i daya kuma, ya zargi kungiyar Hezbollah ta Lebanon da ta yi amfani da fararen hula domin kiyayenta, kuma ta kai hari ga kasar Isra'ila da makaman roka. Ya sanar da cewa, kasar Isra'ila ba za ta tsagaita bude wuta ba, idan ba ta cimma burin soja ba. Kasar Isra'ila za ta ci gaba da murkushe 'yan dakarun kungiyar Hezbollah na kasar Lebanon. Sojojin Isra'ila za su yi kwanaki 10 zuwa 14, domin kammala aikin soja.

Manazarta sun nuna cewa, muhimman dalilan da suke sa kasar Isra'ila ba ta kula da kiran da kasashen duniya suka yi mata, kuma tana tsayawa kan aikin soja da take yi wa kasar Lebanon su ne:

Da farko, ko da ya ke rikicin da ake yi a tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ya riga ya shafe da makonni 3, amma kasar Isra'ila ba ta sami sakamako mai kyau ba. Halin yaki da ake ciki zai nasaba da matsayin da kasar Isra'ila za ta dauka a kai a cikin shawarwarin tsagaita bude wuta, idan an tsagaita bude wuta a yanzu, kasar Isra'ila ba za ta samu kome ba.

Na biyu, bisa matsayinta na abokiyar kawancen kasar Amurka, ba kawai kasar Isra'ila ta yi yakin sabo da kanta ba, har ma ta yi yaki sabo da kasar Amurka. Manazartar kasar Isra'ila sun nuna cewa, sakamakon aikin soja da kasar Isra'ila ta ke yi, zai nasaba da ko kasar Amurka za ta iya shirya makomar kasar Lebanon nan gaba da ke dacewa da moriyar Amurka, ko a'a, bisa tsare-tsaren shirinta.

Manatarta sun nuna cewa, ko da ya ke kasar Isra'ila ta sanar da cewa, za ta ci gaba da aikin soja, amma lamarin kauyen Gana ya matsa wa kasashen Isra'ila da Amurka sosai, kasashen Biyu ba za su iya cimma burinsu cikin sauki ba.

Da farko, lamarin ya harzaka jama'ar kasar Lebanon, haka kuma jama'ar da ke goyon bayan kungiyar Hezbollah sun karu sosai. A sa'i daya kuma, kasar Lebanon ta kara tsaya kan matsayin taurin kai kan matsalar shawarwarin tsagaita bude wuta, gwamnatin kasar Lebanon ta tabbatar da cewa, tilas ne an tsagaita bude wuta ba tare da sharuda ba a farko, bayan haka kuma za a yi shawarwari kan hakikanin matsaloli.

Na biyu, barkewar lamarin kuayen Gana, ta rage matsayin siyasa da kasashen Amurka da Isra'ila ke tsayawa a kai a kasashen duniya, wajen matsalar kasashen Lebanon da Isra'ila. Yanzu, kasashen duniya suna nuna kiyewa ga kasar Isra'ila, kasar Amurka kuma tana fuskantar matsi na iri daban daban, sabo da tana goyon bayan Isra'ila wajen yin yaki.

Lamarin kauyen Gana ya shakku ga kasashen Isra'ila da Amurka kan tsare-tsaren shirin matsalar kasashen Lebanon da Isra'ila. Wannan ya nuna cewa, sakamakon kara rinchabewar rikicin da ake yi a tsakanin Lebanon da Isra'ila, zai sanya tsare-tsaren shirin kasashen Isra'ila da Amurka ya bi ruwa. (Bilkisu)