Bisa labarin da muka samu daga bangaren soja na kasar Sin, an ce, kasar Sin za ta tura jirgin sama na musamman zuwa kasar Isra'ila domin dauko akwatin da ke dauke da gawar Du Zhaoyu, 'dan kallon soja na kasar Sin a MDD, zuwa gidansa kasar Sin.
Bayan da laftanar kanar Du ya mutu a sakamakon farmaki da sojojin sama na Isra'ila suka kai, jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar Sin sun mai da hankali a kan haka, sun bukaci hukumomin da abin ya shafa su shawo kan matsalolin da ke tasowa sakamakon rasuwarsa yadda ya kamata. A ran 27 ga wata, ofishin harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasar Sin ta riga ta aika da kungiyar aiki zuwa Isra'ila domin daidaita wannan matsala.
A ran 30 ga wata, kuhumar sa ido a kan tsagaita wuta ta MDD ta yi bikin jana'izar 'yan kallo 4 na MDD. Mai samun sulhuntawa a kan yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiyya na babban sakataren MDD Alvaro De Soto ya karanta jawabin da Kofin Annan ya rubuta dangane da su. Jakadan kasar Sin da ke Isra'ila Chen Yonglong da kungiyar aiki ta kasar Sin sun halarci bikin.(Danladi)
|