Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-30 21:18:58    
Sabunta: Mutanen Lebanon 51 sun mutu sakamakon hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai kan wani kauyen Lebanon

cri

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na Lebanon suka bayar, an ce, a ran 30 ga wata, dakarun sama na Isra'ila sun tura jiragen sama na yaki sun kai hare-hare kan kauyen Qana daga sararin sama, inda aka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 51, ciki har da yara 22.

Bangaren dakarun Isra'ila ya ce, kauyen Qana yana daya daga cikin sansanonin da masu rike da makamai na Hazbollah suke kai farmaki kan Isra'ila. Kafin sojojin Isra'ila su dauki matakin kai hare-hare kan kauyen Qana, sun riga sun yi wa kauyawan Qana kashedi, inda suka neme su da su janye jikinsu daga kauyen.

Bayan aukuwar matsalar mutane da yawa a kauyen Qana, Mr. Fouad Seniora, firayin ministan kasar Lebanon ya yi tir da matakin da sojojin Isra'ila suka dauka, ya kuma nemi bangaren Isra'ila da ya daina wutar yaki ba tare da kowane sharadi ba nan da nan. Ya kuma shelanta cewa, kafin sojojin Isra'ila su daina kai hare-hare kan Lebanon, bangaren Lebanon ba zai halarci kowane irin shawarwari ba.

Bugu da kari kuma, a wannan rana, Amr Moussa, babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa ya yi tir da matakin kai hare-hare kan kauyen Lebanon da sojojin Isra'ila suka dauka. Ya kuma nemi kafa wata kungiyar kasashen duniya domin binciken wannan matsala. Sannan kuma, ya yi kira ga kasashen Larabawa da su nuna goyon baya ga jama'ar Lebanon.

Bisa labari daban da aka bayar, an ce, madam Condoleeza Rice, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka wadda ke yin ziyara a yankin Gabas ta tsakiya ta nuna bakin cikinta ga hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai kan kauyen Qana. Ta kuma tsai da kudurin cewa za ta dakatar da ziyararta a kasar Lebanon. Bisa shirin da aka tsara, ya kamata ta kai ziyara a kasar Lebanon a yau. Ta bayyana cewa, za ta ci gaba da yin shawarwari da jami'an kasar Isra'ila domin yunkurin kafa sharadin kawo karshen wutar yaki a tsakanin Lebanon da Isra'ila. (Sanusi Chen)