A ran jiya 29 ga wata, ofishin MDD da ke kasar Lebanon ya bayar da sanarwar cewa, a sakamakon rikicin da ke tsakanin kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da Isra'ila, mutane a kalla dai 600 sun mutu, a yayin da wasu fiye da 3,220 suka ji raunuka.
Sanarwar ta ce, sabo da rikicin kuma, mutanen kasar Lebanon kimanin dubu 800 sun bar gidajensu.
A ran nan, an ci gaba da rikicin da ya barke a tsakanin Lebanon da Isra'ila, wanda aka riga aka shafe makonni biyu da samunsa. A ran nan, jiragen saman sojan Isra'ila sun kai harin boma-bomai a kan hanyar da ke tsakanin birnin Beirut, babban birnin Lebanon da kuma birnin Damascus, hedkwatar kasar Syria, sakamakon haka kuma, an sake katse hanyar. Ban da wannan, sojojin Isra'ila sun kuma kai hare-hare a kan yankunan Bint Jbail da Maroun al-Ras da ke kudancin Lebanon. Sansanin Indiya na sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD wanda ke girke a dab da Bint Jbail shi ma ya gamu da farmakin sojojin Isra'ila, inda sojojin Indiya guda biyu suka jikkata.
A ran nan kuma, babban sakataren kungiyar Hezbollah, Said Hasan Nasrallah ya yi barazanar cewa, idan sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai farmaki a kan jama'ar Lebanon, to, dakarun kungiyar Hezbollah za su kai farmaki a kan karin biranen tsakiyar Isra'ila.
Bayan haka, shugaban kasar Lebanon shi ma ya la'anci Isra'ila a kan yunkurinta na neman tayar da yakin basasa a Lebanon.
A wata sabuwa kuma, an ce, a jiya, sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta gana da firaministan Isra'ila a birnin Kudus, inda suka tattauna batun tura rundunar sojojin tarayyar kasa da kasa zuwa yankunan da ke kan iyakar kudancin Lebanon.(Lubabatu Lei)
|