Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-30 18:18:20    
Mutanen Lebanon 51 sun mutu sakamakon farmakin da sojojin Isra'ila suka kai daga sararin sama

cri
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na Lebanon suka bayar, an ce, a ran 30 ga wata, sojojin sama na Isra'ila sun tura jiragen sama na yaki domin kai farmaki daga sararin sama kan kauyen Qana da ke kudancin yankin kasar Lebanon, inda aka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 51, ciki har da yara 22.

Bisa labarin da mutumin da ya ga abin ya faru a kauyen Qana ya bayar, an ce, gidaje da dama tare da wani gini, inda mutane kimanin dari 1 suke zama sun ruguje a cikin farmakin da sojojin Isra'ila suka kai kan kauyen.

Hukumar soja ta Isra'ila ta ce, kauyen Qana yana daya daga cikin muhimman sansanoni, inda masu rike da makamai na kungiyar Hezbollah suke kai farmaki kan Isra'ila. Kafin ta kai farmaki kan kauyen, hukumar sojojin Isra'ila ta riga ta yi wa kauyawan Qana kashedi, ta neme su da su janye jikinsu daga kauyen.

Bayar da aukuwar mutuwar mutane da yawa a cikin farmakin da sojojin Isra'ila suka kai kan kauyen Qana, Fouad Seniora, firayin ministan Lebanon ya yi tir da matakin da sojojin Isra'ila suka dauka, ya kuma nemi bangaren Isra'ila da ya daina wutar yaki nan da nan. Mr. Seniora ya kuma shelanta cewa, kafin sojojin Isra'ila su daina kai farmaki kan Labanon, bangaren Lebanon ba zai halarci kowane irin shawarwari ba.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Lebanon ta riga ta sanar wa Condoleeza Rice, sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka wadda ke yin ziyara a yankin Gabas ta tsakiya, cewar kafin sojojin Isra'ila su daina wutar yaki, bangaren Lebanon ba zai yi shawarwari da ita ba. (Sanusi Chen)