Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-29 21:32:52    
Kasar Isra'ila ta ki amincewa da shawarar dakatar da wutar yaki da M.D.D. ta bayar

cri
A ran 29 ga wata, gwamnatin kasar Isra'ila ta ki amincewa da wata shawarar da M.D.D. ta bayar a ran 28 ga wata. Bisa wannan shawara, M.D.D. tana fatan kasashen Isra'ila da Lebanon za su iya dakatar da yin wutar yaki a tsakaninsu har na tsawon sa'o'i 72 domin hukumomin ba da agaji na kasashen duniya za su iya shiga yankunan rikici domin samar da kayayyakin mutumtaka.

A wannan rana, jaridar Haaretz ta kasar Isra'ila ta tsamo maganar da Avi Pazner, kakakin gwamnatin kasar Isra'ila ya yi, cewar sojojin Isra'ila sun riga sun bude wata hanyar mutumtaka domin za a iya shiga kasar Lebanon daga yankin rikici da ke tsakanin kasashen biyu. Sabo da haka, gwamnatin Isra'ila tana ganin cewa, dakatar da wutar yaki a tsakaninsu har na tsawon sa'o'i 72, wannan ba abu da ya wajaba ba ne.

Sannan kuma, a wannan rana, madam Tzipi Livni, ministar harkokin waje ta kasar Isra'ila ta bayyana cewa, Isra'ila tana da sha'awa ga shawarar bude wata hanyar mutumtaka a Lebanon da kasar Faransa ta bayar. (Sanusi Chen)