A ran 28 ga wata, dakarun rikon kwarya ta M.D.D. da ke Lebanon ya bayar da wata sanarwa, inda aka shelanta cewa, a cikin dan lokaci ne, za a janye wasu 'yan kallo na soja na M.D.D. daga yankunan da ke iyakar Isra'ila da kasar Lebanon.
Wannan sanarwa ta ce, a ran 27 ga wata, sojojin Isra'ila da masu rike da makamai na kungiyar Hezbollah ta Lebanon sun yi ta bude juna wuta har sau da yawa. Bangarorin biyu sun sha bude wutar igwa sau da yawa kan sansanonin dakarun M.D.D. da ke Lebanon. Sakamakon haka, rundunar dakarun M.D.D. da ke Lebanon ta tsai da kudurin cewa, ta janye dukkan 'yan kallonta daga tasoshin sa ido guda 2 da ke garin da ke kudancin kasar Lebanon.
A ran 31 ga wata, za a kawo karshen wa'adin aiki na wannan rundunar soja ta M.D.D. da ke Lebanon. Game da wannan batu, a ran 28 ga wata, Mr. Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya bayyana cewa, yanzu wannan rundunar soja ba ta da sharadin tabbatar da zaman lafiya a kasar Lebanon. Sabo da haka, yana fatan kwamitin sulhu na M.D.D. zai tsawaitar da wa'adin aiki na wannan rundunar soja har na tsawon wata 1 domin za a iya daukar sauran matakai wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin. Bugu da kari kuma, Mr. Annan ya ce, zai gayyaci wakilan wasu kasashe da su je hedkwatar M.D.D. da ke New York a ran 31 ga wata domn halartar taron kafa rundunar soja ta tabbatar da kwanciyar hankali a yankunan Gabas ta tsakiya. (Sanusi Chen)
|