Ran 28 ga wata, kasashen Amurka da Rasha da Sin da Birtaniya da Faransa da Jamus sun gabatar da shirin kuduri kan batun nukiliya na kasar Iran ga kasashe mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda aka bukaci kasar Iran da dole ne ta daina dukan ayyukan tace sinadarin uranium kafin karshen watan Agusta, in ba haka ba, mai yiwuwa ne zai fuskanci takunkumin da kasashen duniya za su garkama mata.
Shirin kudurin ya kalubalanci kasar Iran da ta aiwatar da kudurin da kwamitin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya wato IAEA ya zartas da shi, ya daina dukkan ayyukan da suka nasaba da tace sinadarin uranium da sake gyare shi. Shirin kudurin ya kara da cewa, idan kasar Iran ba za ta aiwatar da kudurin da abin ya shafa ba kafin ran 31 ga wata Agusta, kwamitin sulhu zai yi la'akari da garkama mata takunkumi a fannonin tattalin arziki da diplomasiyya.
Shugaba na wannan wata na kwamitin sulhu kuma zaunannen wakilin kasar Faransa da ke majalisar Mr. Jean-Marc de la Sabliere ya ce, kwamitin sulhu zai kada kuri'a kan wannan shirin kuduri a ran 31 ga wata.
|