Tare da kusantowar shekarar 2008, taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 sai kara jawo hankulan jama'ar kasar Sin da kuma na duk duniya yake yi a kowace rana. A matsayin wani gagarumin taron wasannin motsa jiki na duk duniya, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun mai da hankali sosai kan wannan kasaitaccen taro kuma suna fatan ' yan wasa na kasar za su samu sakamako mai gamsarwa a gun taron wasannin. Yanzu sassan kula da ayyukan wasanni iri daban daban na kasar Sin suna nan suna aiki tukuru wajen shirya horon wasanni musamman ma na kwallon tenis, wanda a da aka yi biris da shi cikin ayyukan wasanni masu rinjaye na kasar kafin haka 'yan wasa sun yi fintinkau wajen samun lambar zinariya a gun irin wannan wasa tsakanin mata bibbiyu a Aden.
Yanzu, an tabbatar da, cewa wasan kwallon tenis na kasar Sin na kan hanyar zama ta sana'a domin taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a shekarar 2008 a nan Beijing.
Mr. Jiang Hongwei mai shekaru 49 da haihuwa, babban malamin koyarwa ne na kungiyar wasan kwallon tenis ta mata na kasar Sin. Yanzu yana jan ragamar kungiyar wasan kwallon tenis ta mata na kasar Sin zuwa taron wasannin Olympics na Beijing. A shekarar 1992, Mr. Jiang Hongwei ya taba jagorancin kungiyar wasan kwallon tenis ta mata na kasar Sin ga shiga taron wasannin motsa jiki na Olympics na Barcelona.
An tuna da, cewa yau da shekaru sama da goma da suka shige, wasan kwallon tenis na mata na kasar Sin ya taba hawa kan matsayin ci gaba. Amma, a wancan lokaci, ba hanyar sana'a ake bi daga dukkan fannoni ba wajen gudanar da harkokin wasan kwallon tenis, wato ke nan ' yan wasan kwallon tenis na kasar Sin sun kasa samun damar shiga gasannin sana'a na ATP da na WTA. Saboda haka, sakamakon da ' yan wasan suka samu bai kai a zo a gani ba. Amma, bayan shekaru sama da goma, halin ya canja. Mr. Jiang Hongwei ya bayyana muhimman tsare-tsaren wasan kwallon tenis na kasar Sin a kan cewa: 'Me ya sa muke nacewa ga bin hanyar sana'a wajen gudanar da wasan kwallon tenis ? Dalili shi ne idan muka yi watsi da hanyar sana'a, to labuddah da kyar 'yan wasan kwallon tenis za su cimma manufar samun sakamako mai gamsarwa a taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing.'
Kamar yadda Mr. Jiang Hongwei ya fada, cewa yanzu wasan kwallon tenis na kasar Sin na kan hanyar zama ta sana'a cikin taka tsan-tsan. Mutane ba su manta ba, kafin taron wasannin motsa jiki na Olympics na Aden, tuni ' yan wasan kasar Sin sun samu babban ci gaba wajen gagarumar gasa da aka yi a wancan shekara ,wato sun shiga cikin jerin ' yan wasa mata guda 8 masu karfi dake halartar budaddiyar gasar wasan kwallon tenis tsakanin mata bibbiyu da aka yi a Australiya, lallai wannan ya aza harsashi mai inganci ga ' yan wasa na kasar Sin wajen samun lambar zinariya a gun taron wasannin Olympics na Aden. Bayan wannan lokaci, wasan kwallon tenis na kasar Sin ya kuma shiga wani lokaci daban na zinariya, su Zhenjie da Yanzi wato ' yan wasan kwallon tenis tsakanin mata bibbiyu sun samu lambar zinariya ta farko a budaddiyar gasa na wasan kwallon tenis na shekarar 2006 da aka yi a kasar Australiya ; Ban da wannan kuma, ba a tafi an bar ' yan wasan kwallon tenis tsakanin mace da mace baya ba, Miss. Lina da Mr.Zhenjie sun samu lambar zinariya ta farko daya bayan daya a gasar da aka yi ta sauya zango ta WTA ; musamman ma ' yar wasa mai suna Pengshuai wadda shekarunta ba su kai 20 da haihuwa ba ta fi nuna gwaninta har sau tari ne ta lashe 'yan wasa mata dake kan matsayin gurabe goma na farko a duniya a gun irin wannan wasa.
Amma duk haka, Mr. Jiang Hongwei ya gane, cewa lallai za a gamu da wahaloli kan wannan sabuwar hanyar zama ta sana'a da ake bi zuwa taron wasannin Olympics na Beijing. Ya furta, cewa :' Yanzu mutane na zura ido sosai kan kungiyarmu bayan da muka samu lambar zinariya a taron wasannin Olympics, wato ke nan sun soma nazarin dabarun yin wasa da muka samu. Don haka, wajibi ne mu kyautata dabarunmu na muhimman tsare-tsare'.
Bayan da aka shafe shekaru fiye da l0 ana bunkasa wasan kwallon tenis a kasar Sin, sai Mr. Jiang Hongwei ya ji a zuciyarsa, cewa :
'Hanyar zama ta sana'a da wata kasa take bi wajen gudanar da harkokin wasan kwallon tenis da kuma daguwar matsayin wasan da ta samu suna da nasaba sosai da babban karfin da wannan kasa take da shi a fannin tattalin arziki. Yanzu, kasarmu ta samu bunkasuwa da ci gaba. Wannan dai ya zama tamkar karfin ingizawa ne ga kara yalwata wasan kwallon tenis'.( Sani Wang )
|