Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-27 20:55:37    
Kasar Sin ta kara sa ido kan ingancin kayayyakin da ake fitar da su zuwa kasashen waje

cri
A ran 27 ga wata, wani jami'in hukumar sa ido da binciken ingancin kayayyaki ta kasar Sin ya ce, hukumar tana daukar matakai kan yadda za a sa kaimi kan masana'antu da kara kyautata ingancin kayayyakin da suke fitar da su zuwa kasashen waje. A sa'i daya kuma, za ta kara sa ido kan ingancin kayayyakin shigi da fici a tasoshin bincike na kasar domin tabbatar da ingancin kayayyakin da ake shigo da su a kasar Sin.

Yanzu, kasar Sin kasa ce wadda take gaba kan sana'o'in kira. Yawan babura da akwatunan talibijin da kasar Sin take kerawa yana matsayin farko a duk fadin duniya. A sa'i daya kuma, kasar Sin tana sayar da kayayyakin wasan yara da na lantarki na gida da tufafi a kasuwannin kasashen duniya da yawa. Amma, wasu masana'antun kasar Sin suna fitar da kayayyakinsu marasa inganci. Sakamakon haka, sun yi tasiri sosai ga ingancin kayayyakin kasar Sin. Mr. Pu Changcheng, mataimakin shugaban hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin ya ce, yanzu gwamnatin kasar Sin tana kokari wajen daidaita wannan matsala. "Yanzu kasar Sin muhimmiyar kasa ce wajen sana'o'in kira, amma a sa'i daya kuma, kasar Sin kasa ce mai tasowa. Ingancin kayayyakin kasar Sin yana da bambanci sosai idan an kwatanta su da na kasashe masu ci gaba. Bugu da kari kuma, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasuwa sosai a cikin gajeren lokaci. A hakika dai, ya kasance da matsaloli iri iri game da ingancin kayayyaki. Wannan kuma muhimmiyar matsala ce da gwamnatin kasar Sin za ta kara sa ido kuma za ta yi kokarin kawar da su."

A waje daya kuma, kasar Sin ta dauki matakan yanke hukunci da sa kaimi kan masana'antu domin kyautata ingancin kayayyakin da suke kerawa. Alal misali, a wasu masana'antun kera kayayyakin lantarki, an dauki matakin rashin binciken ingancin kayayyakin da wasu masana'antu suke kerawa domin ingancin kayayyakin da suke kerawa yana da kyau a kullum.

Bugu da kari kuma, lokacin da ake fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, hukumar sa ido da kuma binciken ingancin kayayyaki ta kasar Sin ta kara karfin binciken ingancinsu a tashar bincike. Mr. Pu ya ce, "Mataki daban da muke dauka shi ne a tasoshin bincike, mun kara sa ido kan ingancin kayayyakin da ake fitar da su zuwa kasashen waje. Idan mun ga akwai kayan jabu ko ingancin kayayyaki bai kai ma'aunonin kasar Sin ba, ko mun ga kayayyakin da ake shigowa da su a kasar Sin suna kamuwa da kwayoyin cuta, shi ke nan, mun daina ba su izinin fici ko shigi. Bisa kididdigar da aka yi, a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan darajar kayayyakin da ingancinsu bai kai ma'aunonin kasar Sin ba kuma ba su samu izinin fita ba ya kai kudin dolar Amurka biliyan 11."

Mr. Pu Changcheng ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta dauki ma'aunoni daban ga kamfanonin kasashen waje, ciki har da sassansu a nan kasar Sin ba. Dole ne ingancin kayayyakin da suke kerawa kuma suke fitar da su zuwa kasuwannin kasashen waje ya kai ma'aunonin kasar Sin, hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin za ta sa ido da kuma yin bincike a kansu. Mr. Ge Zhirong, shi ma mataimakin shugaban hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin, ya ce, "A cikin farkon rabin shekarar da muke ciki, bayan da aka ga ingancin kayayyakin da kamfanonin kasashen waje suka kera, kuma suke shigowa da su a kasuwar kasar Sin bai kai ma'aunonin kasar Sin ba, hukumar sa ido kan ingancin kayayyaki ta kasar Sin ta riga ta daina bai wa wadannan masana'antun kasashen waje izinin fitar da kayayyakinsu a kasuwannin kasar Sin har sau da yawa. Lokacin da masana'antun kamfanonin mallakar kasashen waje da ke nan kasar Sin suke fitar da kayayyakinsu zuwa sauran kasashen duniya, dole ne ingancin kayayyakinsu ya biya bukatun ma'aunonin da kasar Sin ta tsara. Idan ba su biya bukatun ma'aunonin kasar Sin ba, shi ke nan, ba za su samu izinin fitarwa ba." (Sanusi Chen)