Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 21:14:23    
Taron duniya na Rome bai sami ra'ayi daya kan shawo kan rikicin kasashen Lebanon da Isra'ila ba

cri
Ran 26 ga wata, a birnin Rome, hedkwatar kasar Italiya, taron duniya kan batun Gabas ta Tsakiya bai sami ra'ayi daya kan shawo kan rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila ba.

A gun bikin bude taron da aka yi a ran nan, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Kofi Annan ya bukaci kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da kasar Isra'ila da su daina daukan matakan soja nan da nan. Ya kuma jaddada cewa, dole ne bangarorin kasashen Lebanon da Isra'ila su tabbatar da tsagaita bude wuta nan da nan, in ba haka ba, ba za a yi ayyukan akidar jin kai yadda ya kamata ba. Ban da wannan kuma, firaministan kasar Italiya Mr. Romano Prodi ya bayyana cewa, kasar Italiya tana goyon bayan shawarar da Mr. Annan ya bayar kan girke sojojin duniya a bakin iyakar kasashen Lebanon da Isra'ila. Bangarorin da abin ya shafa suna bukatar samun ra'ayi daya kan kafa hanyar akidar jin kai, ta yadda za a kai wa kayayyakin ba da agaji a kasar Lebanin lami lafiya. Saboda taron bai sami ra'ayi daya kan batutuwan da abin ya shafa ba, shi ya sa, bayan taron, bi da bi ne bangarorin da abin ya shafa sun bayyana cewa, za su ci gaba da neman samun dabarar shawo kan rikicin kasashen Lebanon da Isra'ila.(Tasallah)