Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-26 20:36:26    
An rufe taron duniya kan sa aya ga rikicin kasashen Lebanon da Isra'ila a Rome

cri
Ran 26 ga wata, a birnin Rome na kasar Italiya, an rufe taron kasa da kasa kan sa aya ga rikicin da ke tsakanin kasashen Lebanon da Isra'ila. A gun bikin bude taron, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Kofi Annan ya bukaci kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon da kasar Isra'ila da su daina daukan matakan soja nan da nan.

A gun bikin bude taron da aka yi a ran nan, Mr. Annan ya bukaci kungiyar Hexbollah ta kasar Lebanon da ta daina harba rokoki ga fararen hula na kasar Isra'ila, a sa'i daya kuma, ya yi kira ga kasar Isra'ila da ta daina kai hare-haren bama-bamai da daukan matakan soja ga kasar Lebanon. Ya kuma jaddada cewa, dole ne bangarorin kasashen Lebanon da Isra'ila su tabbatar da tsagaita bude wuta nan da nan, in ba haka ba, ba za a yi ayyukan bayar da jin kai yadda ya kamata ba.

Ban da wannan kuma, firaministan kasar Italiya Mr. Romano Prodi ya jaddada cewa, makasudin kiran wannan taron kasa da kasa shi ne domin mayar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Lebanon, da kuma tabbatar da tsaron kai na kasar Isra'ila.(Tasallah)